Zanga-zanga Ta Barke a Kudancin Najeriya Kan Hukuncin Zaben Kano, Sun Tura Sako Ga Tinubu
- Yayin da ake dakon hukuncin shari'ar zaben Kano, 'yan Arewa a Kudancin Najeriya sun yi zanga-zanga
- Kungiyar 'yan Arewa da ke Kudancin kasar sun shawarci Tinubu da ya tabbatar an yi adalci yayin yanke hukuncin
- Kungiyar ta kuma bukaci a bar wa Gwamna Abba Kabir kujerarshi don samar da zaman lafiya a jihar da ma Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - 'Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi zanga-zanga kan shari'ar zaben jihar Kano.
Kungiyar Arewa ta gudanar da zanga-zangar ce a birnin Ibadan da ke jihar Oyo inda ta ce ana son tuge wanda al'umma su ka zaba.
Mene ma su zanga-zangar ke cewa?
Mataimakin shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum reshen jihar, Shehu Idris ya koka kan halin da ake ciki a yankin Arewa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabar mata a kungiyar, Aisha Isma'il ta ce yadda ake hukunta manyan 'yan siyasar yankin zai kara jefa ta cikin mawuyacin hali.
Kungiyar ta kirayi Shugaba Tinubu da ya saka baki wurin tabbatar adalci a shari'ar da ake yi, cewar Vanguard.
Ta kuma bukaci Tinubu da APC da kada su yi kokarin juya shari'ar zaben jihohi zuwa bangarensu.
Masu zanga-zangar sun yi kira na musamman kan shari'ar jihar Kano inda su ka bukaci a yi hukuncin adalci a Kano saboda duk abin da ya shafi jihar zai taba Arewacin Najeriya.
Wane shawara ma su zanga-zangar su ka bayar?
Shehu Idris ya ce:
"Ana son yin fashi da tsakar rana kan hukuncin kotu inda ake kokarin kawo cikas kan abin da mutane su ka zaba."
Yayin da Aisha Isma'il ta bukaci Tinubu da ya ji bukatun mata kan yin adalci a shari'ar Kano.
Ta ce:
"Duk lokacin da giwaye ke fada, ciyawa ce ke shan wahala, mu na son a bar Abba Kabir a kan kujerarshi."
Kotu ta yi hukunci kan rusau a Kano
A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rusau da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar.
Kotun ta rufe asusun bankunan jihar guda 24 wanda masu karar ke bukatar diyyar biliyan 30.
Asali: Legit.ng