Sabon Rikici Ya Kunno Kai a PDP Yayin da Aka Dakatar da Shugaban Jam’iyya, Karin Bayani

Sabon Rikici Ya Kunno Kai a PDP Yayin da Aka Dakatar da Shugaban Jam’iyya, Karin Bayani

  • PDP ta sake shiga matsala yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Imo suka dakatar da shugabanta na jihar, Injiya Charles Ugwu
  • An dakatar da Ugwu ne bayan manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun nuna rashin karfin gwiwa a kansa
  • Dakatarwar Ugwu na zuwa ne bayan shugaban ciyamomin kananan hukumomi na PDP ya gabatar da wani kudiri a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Imo - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana fama da wani rikicin cikin gida yayin da aka dakatar da shugabanta a jihar Imo, Injiniya Charles Ugwu.

An dakatar da Ugwu ne bayan wani kudiri da shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Ohaji Egbema kuma shugaban ciyamomin jam’iyyar na jihar, Hon Emeka Alihe ya gabatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Bayan Alihe ya gabatar da kudirin, sai shugaban jam’iyyar PDP na Owerri Municipal, Hon Godspower Apollos ya mara masa baya, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Sabon rikici ya kunno kai a PDP
PDP Ta Fada Sabon Rikici Yayin da Aka Dakatar da Shugaban Jam’iyya, Karin Bayani Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin ciyamomin da suka goyi bayan tsige shugaban PDP na jihar Imo

Akalla shugabannin kananan hukumomi 18 da mambobin kwamitin zartarwa na Jiha ne suka amince da kudirin dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na jihar ta Imo.

An tattaro cewa an dakatar da Ugwu ne bisa zargin saba ka'ida da kuma rashin biyayya.

An nada shugaban jam’iyyar na shiyyar Okigwe, Chidi Dike a matsayin shugaban riko na jam’iyyar na jiha.

Rikicin PDP ya girmama a Imo yayin da aka tsige shugaban jam'iyya

Hakan na kunshe a cikin wata wasika da jam'iyyar reshen jihar ta saki bayan taronta inda ta nuna rashin kwarin gwiwa a kan Ugwu.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Sakataren jam’iyyar na jiha, Hon Njaba Duruiheoma da Emeka Alihe, jigo a jam’iyyar ne suka sanya wa wasikar hannu, inda suka bukaci a gaggauta dakatar da Injiniya Charles Ugwu daga ofis.

Ya ce shugaban jam’iyyar ya gaza kiran taron kwamitin ayyuka na jiha wanda ya yi karo da tanadin S. 21 (3) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A cewarsam Injiniya Ugwu ba shi da wani kwakkwaran dalili na kin halartan kowani taron godiya da dan takarar gwamnan jam'iyyar, Sanata Samuel Anyanwu, ya kai kananan hukumomi 27 na jihar.

Sun kuma yi nuni da cewa Injiniya Ugwu bai halarci taron godiya na karamar hukumar Owerri Municipal da aka gudanar a sakatariyar jam'iyyar na jihar ba, wanda ya saba sashi na 58(i) (e) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar duk da cewa an sanar da shi batun ziyarar.

Wani jigon jam’iyyar, Honarabul John Diala wanda ya zanta da wakilinmu ya bayyana cewa, "ya kamata ace an dakatar da shi kafin yanzu amma aka dakata har zuwa bayan zabe domin gudun kada mutane su ba shi wata fassara na daban."

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Shugabannin NNPP sun juyawa Abba baya

A wani labari na daban, mun ji cewa sasu shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun juyawa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya, sun goyi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

A cewar jam'iyyar, Abba Gida-Gida bai zama cikakken mamban NNPP ba a lokacin da aka yi zaɓe kamar yadda kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng