Wasu Jiga-Jigan NNPP Sun Kara Jefa Gwamna Abba da Kwankwaso Cikin Babbar Matsala, Gaskiya Ta Bayyana
- Wasu korarrun mambobin NNPP na neman sake jawo wa Gwamna Abba Kabur Yusuf da Kwankwaso matsala
- Sun fito suna yaɗa cewa Abba ba ɗan NNPP bane kuma an kori Kwankwaso, amma jam'iyyar ta fito ta bayyana gaskiya
- Mamban kwamitin gudanarwa (NWC), Ladipo Johnson, ya ce ikirarin da tsoffin jiga-jigan NNPP suka yi ba gaskiya bane
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce wasu korarrun ‘ya’yan jam’iyyar na kokarin yada labaran karya kan Gwamna Abba Yusuf na Kano da Rabiu Kwankwaso.
Mamban kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), Ladipo Johnson, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya yi zargin cewa wasu korarrun mambobin NNPP ƙarƙashin jagorancin Tope Aluko sun fara yaɗa ƙaryar cewa Gwamna Abba ba ɗan jam'iyya bane lokacin da ya tsaya takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma Mista Jonson ya ce tawagar korarrun suna yaɗa cewa NNPP ta kori Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Menene gaskiyar wannan magana?
Amma Mista Jonson ya bayyana cewa dukkan waɗanda bayanan da suke yaɗawa, "karya ce mara tushe balle makama."
A kalamansa ya ce:
"Mun samu rahoton cewa wasu tsirarun korarrun mambobin NNPP ciki harda Tope Aluko da wasu tsoffin shugabannin jihohi sun kira taron yan jarida a Abuja suna yaɗa farfaganda."
"Suna yaɗa cewa mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ba ɗan NNPP bane lokacin da ya tsaya takara da kuma cewa an kori Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam'iyya."
"Wannan karya ce mara tushe, muna da tabbacin Abba Gida-Gida cikakken ɗan NNPP ne a lokacin zaɓe kuma mun yi imani kotun kolin Najeriya zata yi adalci."
Daga ƙarshe, Jonson ya yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su kauracewa kalaman waɗannan mutanen da ba su ƙaunarsu.
"Muna tunatar da jama’a cewa Cif Boniface Aniebonam daya daga cikin wadanda suka kafa NNPP ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf inda ya nemi a tabbatar masa da nasarar da ya samu," in ji shi.
Majalisa Ta Dakatar 'Yan Majalisa Huɗu a Benue
A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da mambobi guda huɗu kan faɗa da yan majalisa masu goyon bayan Gwamna Alia.
Wannan matakin ne zuwa ne yayin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar.
Asali: Legit.ng