Tazarce: Kungiyar APC Ta Fara Nema Wa Tinubu Kuri’u Gabanin Zaben 2027

Tazarce: Kungiyar APC Ta Fara Nema Wa Tinubu Kuri’u Gabanin Zaben 2027

  • An kaddamar da shugabannin sabuwar kungiyar jam'iyyar APC mai suna All Progressives Congress Grassroot Movement (CAGRAM)
  • Kungiyar CAGRAM ta sha alwashin nemawa shugaban kasa Tinubu kuri'u a gabanin zaben 2027 da zai ba shi damar yin tazarce
  • A cewar kungiyar, a watanni shida na shugabancin Tinubu, Najeriya ta samu babban sauyi wanda ya jawo mata martaba a idon duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wata kungiyar APC mai suna 'Consolidated All Progressives Congress Grassroot Movement (CAGRAM)' ta ce ta fara bi lungu da sakuna don nema wa Tinubu Kuri'u gabanin zaben 2027.

Shugaban kungiyar CAGram Engr. Salisu Magaji ya bayyana hakan a wajen kaddamar da shugabannin kungiyar na kasa, shiyyoyi da jihohi a Abuja.

Kara karanta wannan

An nemi Kotun Koli ta tsige Shugaba Tinubu yayin da aka fara wata sabuwar shari'a

CAGRAM/APC/Tinubu
Kungiyar CAGRAM ta ce ta fara bi lungu da sakuna don nema wa Tinubu Kuri'u gabanin zaben 2027. Hoto: CAGRAM
Asali: UGC

Ya bayyana cewa kungiyar za ta yi duk mai yiyuwa don ganin nasarar Tinubu da jam'iyyar APC yayin da kuma yake jinjinawa shugaban kasar kan ayyukan da ya ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar, wacce ta kunci 'yan a mutun Tinubu, ta kuma yaba kan irin nasarorin da jam'iyyar APC ta cimma tsawon shekarun nan.

Shugaba Tinubu ba shi da uban gida a siyasa, kungiyar CAGRAM

Magaji ya kuma bayyana cewa Tinubu ya nuna kyakkyawan tsari na shugabanci, wanda ya jawo wa kasar daraja a idanun kasashen duniya, Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

"Za mu fara bi lungu da sako don nemawa APC kuri'u gabanin zaben 2027, ba za mu yi kasa a guiwa ba har sai mun kawo wa dan takararmu nasara.
"A tsawon watanni shida da hawansa mulki, kowa ya ga irin kamun ludayinsa, an samu nasarori masu tarin yawa, ko a hakan, mun shaida cancantarsa."

Kara karanta wannan

Lauyoyi sama da 200 sun shirya tsaf don tabbatar da Abba Gida-Gida ya yi nasara a kotu

Magaji ya kara da cewa:

"Asiwaju Boka Ahmed Tinubu ne kawai dan takarar da ba shi da uban gida, ba ya kwaikwayon kowa saboda shi ne uban gidan kowa a siyasa. Don haka za mu goyi bayansa dari bisa dari."

The Guardian ta ruwaito sakataren CAGRAM na kasa, Hon. Butches Emmanuel Nwosu, ya godewa mahalarta taron tare da jaddada muhimmancin kishin jam'iyyar APC a zukatansu.

Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna

A wani labarin na daban, shugaba Tinubu ya bayar da umurnin yin bincike biyo bayan wani harin bam da rundunar soji ta kai kan wasu masu maulidi a Kaduna.

Da ya ke jajantawa al'ummar garin Tudun Biri da lamarin ya shafa, Tinubu ya kuma nuna kaduwarsa matuka kan mutuwar mutanen, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.