Dirama Yayin da Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Gagara Magana da Yarensu, Ya Nemo Mai Fassara

Dirama Yayin da Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Gagara Magana da Yarensu, Ya Nemo Mai Fassara

  • An tafka abun kunya yayin da dan takarar gwamnan PDP ya gagara magana da yarensu yayin da ya ke jawabi a gaban dubban jama'a
  • Dan takarar, Asue Ighodalo wanda ake sa ran shi zai gaji Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo sai da ya nemo mai fassara don isar da sako
  • 'Yan Najeriya sun yi ta cece-kuce kan wannan lamari inda su ka ce ai bai dace da mulkinsu ba yayin da wasu ke cewa ba yare ake bukata ba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Edo ya nemi taimakon mai fassara yayin da ya ke jawabi ga kabilar Esan, cewar PM News.

Kara karanta wannan

Ni na fatattaki Shekau da Qaqa, da yanzu Niger ta zama hedikwatar Boko Haram, tsogon gwamna Aliyu

Asue Ighodalo wanda ake sa ran shi ne zabin Gwamna Godwin Obaseki a zaben da za a gudanar a 2024 ya bayyana cewa shi dan asalin kabilar Esan ne.

An yi abin kunya yayin da dan takarar gwamna ya gagara jawabi da yarensu
Asue Ighodalo ya nemi mai fassara yayin da ke jawabi ga 'yan kabilarshi. Hoto: Godwin Obaseki, Asue Ighodalo.
Asali: Facebook

Wane taimako Ighodalo ya nema?

Yayin da ya ke jawabi, Ighodalo ya nemi mai masa fassara yayin da ya gagara yin magana da yaren da ya ke ikirarin ya fito, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ighodalo yayin da ya ke mai da martani kan cece-kucen da ake yi, ya ce shi ainihin Esan ne amma a jihar Legas ya tashi.

Dan takarar wanda ma'aikacin banki ne ya yi magana da Turanci a gaban 'yan kabilarshi a kauyen Ewohimi da ke karamar hukumar Esan ta Gabas.

Mene Ighodalo ke cewa?

Ya bukaci neman mai fassara zuwa yaren Esan inda ya ke cewa:

"Komai nawa ina yin shi ne a yankin Esan, saboda ba mu da tashin hankali, mahaifiyata ta na nan, ni asalin dan kabilar Esan ne.

Kara karanta wannan

Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta

"Ba zan yi amfani da kalmar dan gida ba saboda mutane sun yi amfani da shi da yawa, ni dan kabilar Esan ne na ainihi."

Shaibu ya bayyana matsayarsa kan takara

A wani labarin, mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya bayyana aniyarshi ta tsayawa takara a zaben shekarar 2024.

Shaibu ya bayyana cewa yadda ya fito babu mai ya dakatar da shi saboda kudurori masu kyau da ya ke da shi a jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da Shaibu ke takun saka da uban gidansa, Gwamna Godwin Obaseki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.