Rikicin Shari’ar Kano: An Kai Karar Gwamna Yusuf Majalisar Dinkin Duniya, Bayani Ya Fito
- Tirka-tirkar da ke faruwa a jihar Kano kan shari'ar gwamnan jihar ta dauki wani sabon salo, yayin da lamarin ya tsallaka zuwa kasashen ketare
- A ranar Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta karbi wani korafi tare da neman Majalisar ta binciki Gwamna Abba Kabir Yusuf
- An zargi gwamnatin jihar Kano da rura wutar rikici a jihar sakamakon ci gaba da farmakar fannin shari'a da ya ke yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Kungiyar matasa 'yan kasuwa na jami'ar APC na Kano (APC-YBCK) ta gudanar da zanga-zanga a ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja a ranar Juma'a.
A yayin zanga-zagar, sun nemi majalisar ta sanya takunkumi akan gwamantin jihar Kano da magoya bayanta, inda suke zargin ana farmakar fannin shari'a.
Me ya faru bayan hawan NNPP mulki a Kano?
Kungiyar ta kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta amince wa fannin shari'ar Najeriya ya rinka gudanar da ayyukansa ba tare da sa hannun wasu daga waje ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bisa jagorancin Alhaji Umar Lafiya, kungiyar matasan APC ta kuma gabatar da takardar korafi akan Gwamna Abba Yusuf, Legit ta ruwaito.
Sun yi ikirarin cewa tun da jam'iyyar NNPP ta hau mulki a Kano, duk harkokin kasuwanci suka durkushe a kasar.
Korafi akan Gwamna Abba Yusuf
Biyo bayan wannan korafi da suka gabatar mai taken "Dole dokar shari'a ta tabbata" ga ofishin UN, Alhaji Ladiyo ya zanta da manema labarai, inda ya yi Allah wadai da rushe-rushen gine-ginen mutane da gwamnatin Kano ta yi.
Ya yi ikirarin cewa ba a bi ka'ida wajen rusa gine-ginen ba, wanda hakan ya kashe kasuwanci da rayuwar 'yan kasuwa a jihar.
Kungiyar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki gwamnatin Abba kan rusa dukiyoyin al'umma.
Hakazalika Alhaji Ladiyo ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta mayar da hankali kan gina al'ummar kasar da tsaya wa rushe-rushen dukiyar jama'a.
Kotu ta garkame matar da ta lakadawa mijinta duka a Kano
A wani labarin, wata mata da ta lakadawa mijinta dukan kawo wuka a Kano ta fuskanci hukuncin kotun majistire da ke Rijiyar Lemu, Legit Hausa ta ruwaito.
An gurfanar da matar ne mai suna Hafsa bisa zarginta da yi wa mijinta dukan tsiya kan zargin yana hira da 'yan mata a waya.
Asali: Legit.ng