Takardu 1,800 Ne Aka Samu Babu Sa Hannu, Kotu Ta Zaftarewa Abba Kuri’u 16,5000 – Lauya
- Wole Olanipekun, SAN ya gabatar da korafin da ake sa rai za su sa Abba Kabir Yusuf ya tsira da kujerarsa
- Babban lauyan ya fadawa Kotun Koli cewa an yi kuskure a wajen raba NNPP da kuri’u 165,616 da ta samu
- Olanipekun ya ce mafi yawan wadannan kuri’u da aka duba, su na dauke da sa hannu da kuma hatimin INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Wole Olanipekun, SAN ya daukaka shari’a a kotun koli, ya na kalubalantar tsige Abba Kabir Yusuf da aka yi a kotun daukaka kara.
Daily Nigerian ta ce Wole Olanipekun, SAN wanda shi ne shugaban lauyoyin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da korafi gaban kotun.
An tsige gwamnan na Kano ne bisa rashin sa hannu a wasu takardun kada kuri’u, saboda haka aka zaftarewa jam’iyyar NNPP kuri’u 165,616.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuri'un Abba/NNPP 165,616 na bogi ne?
Babban lauyan ya shaidawa Kotun Koli shaidan da APC ta kira a kotun zabe, ya iya tabbatar da kuri’u 1, 886 aka samu babu sa hannu.
Olanipekun ya yi ikirarin cewa hujja mai lamba P169 da Aminu Harbau ya gabatar ba su nuna NNPP ta na da haramtattun kuri’u 165,616 ba.
Lauyan yake cewa shaidan APC ya iya nunawa kotun korafin zabe cewa daga cikin kuri’u 165,616 da aka duba, 3,936 rak ne marasa sa hannu.
Korafin lauyan Abba Yusuf a kotun koli
"Hujja ta P169 ta tabbatar da cewa takardun kuri’u 3,936 ne aka samu babu sa hannu, amma an sa kwanan wata da kuma hatimi.
Hujja ta P169 ta tabbatar da cewa takardun kuri’u 1, 886 wanda su ka dauki kashi 1.13% na kuri’un ne kurum ba su da yardar hukuma.
Hujja ta P169 ta tabbatar da cewa 88.33% na takardun kuri’un da aka duba watau 146, 292, duk sun samu sa hannu da kuma hatimi."
- Wole Olanipekun, SAN
Abba zai kalubalanci shaidar jam'iyya
Bayanan lauyan sun nuna akwai kuri’u 6,824 da sa hannu kurum aka yi, 4,347 su na da hatimin INEC sai 2,450 da aka sa hannu da kwanan wata.
Bayan haka, takardun kuri’un su na dauke lamba, tambarin INEC da tutan Najeriya, kuma ya ce an yi kuskure a kan batun zaman Abba ‘dan NNPP.
Bayan rudanin da shari’ar ta kawo saboda kuskure a takardun CTC, an garzaya kotun koli domin rusa nasarar da alkalai su ka ba Nasiru Gawuna.
Hukuncin kotun ya jawo zanga-zanga a Kano da wasu biranen Najeriya kamar Abuja.
Asali: Legit.ng