Ka Jira Ka Ga Makomarka Tukunna, APC Ta Tura Zazzafan Gargadi Ga Abba Kabir Kan Zargin Abu 1 Tak
- Yayin da ake ci gaba da jiran hukuncin kotun koli, jam’iyyar APC ta caccaki Gwamna Abba Kabir kan daukar nauyin masu zanga-zanga
- Tsohon kwamishina a jihar, Musa Ilyasu Kwankwaso shi ya bayyana haka inda ya ce Gwamna Abba Kabir tun farko bai ci zabe ba
- Kwankwaso ya ce gwamnan na asarar kudaden jihar wurin daukar nauyin zanga-zanga madadin ya jira ya ga makomarshi a kotun koli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ta tura zazzafar gargadi ga Gwamna Abba Kabir kan lalata kudaden jihar.
Jam’iyyar ta tura sakon ne a yau Alhamis 3 ga watan Nuwamba yayin da ake jiran shar’ar zaben gwamnan jihar a kotu, Legit ta tattaro.
Wane zargi APC ke yi a Kano?
APC ta zargi Yusuf ta daukar nauyin zanga-zangar da ake yi wurin talauta jihar yayin da kujerarshi ke rawa a kotun koli, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ilyasu Musa Kwankwaso, tsohon kwamishina a jihar shi ya gargadi Yusuf da ya bari a gama hukunci shari’ar a kotun koli tukunna.
Kwankwaso ya ce babu wanda zai fito ya yi zanga-zanga don Abba Kabir ya fadi zabe saboda yadda ya rusa wa al’umma dukiyoyinsu.
Ilyasu ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Kano inda ya gargadi gwamnan kan zanga-zangar da ke faruwa a jihar.
Ya ce:
“An yanke hukunci irin na kotun zabe inda aka tabbatar Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin zabe."
Wane shawari APC ta bayar?
Ya kara da cewa:
“Jam’iyyar NNPP ta na yada farfaganda cewa Kano na cikin wani mummunan hali inda ta ke daukar nauyin masu zanga-zanga a jihar.
“NNPP ta na asarar kudaden jihar Kano wurin neman yardan mutane, ya kamata su jira hukuncin kotun koli tukunna kafin ci gaba da kashe kudaden jihar.”
Kwankwaso ya kara da cewa wannan alamu ne na cewa karshensu ya zo, shi yasa su ke son ta da zaune tsaye a cikin al’umma.
Abba Kabir ya kawo dauki ga mahaukata a Kano
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin kwashe dukkan mahaukatan da ke yawo a titunan Kano.
Gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun korafi daga jama’a kan yadda mahaukatan su ka cika titunan birnin.
Asali: Legit.ng