Kasafin 2024: Jam’iyyar SDP Ta Shirya Yin Aiki da Tinubu Don Ci Gaban Najeriya
- Jam'iyyar SDP ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu tare da yakinin Najeriya za ta samu ci gaba nan gaba kadan
- Jam'iyyar ta kuma jinjinawa Shugaba Tinubu kan mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da farfado da tattalin arziki
- A cewar jam'iyyar, kasafin kudin 2024 da shugaban ya gabatar ya haska manufar gwamnatinsa na sanya 'yan Najeriya farin ciki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta ce kudirin kasafin kudin shekarar 2024 na shugaban kasa Bola Tinubu na Naira tiriliyan 27.5 ya ba 'yan Najeriya kwarin guiwa kan sabuwar Najeriya.
Sakataren shiyyar Kudu maso Yamma na jam’iyyar, Mista Femi Olaniyi, ya shaida hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Alhamis a Legas.
Olaniyi ya bayyana cewa dole ne a samu canji daga kasafin kudin da aka saba gabatarwa a baya ba tare da ya yi tasiri ga ci gaban kasar ba, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da SDP ta ce kan kasafin 2024
Ya kuma yabawa yadda Shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan harkokin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar.
Olaniyi ya ce shirin shugaban kasa na magance rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki da fatara abin a jinjina masa ne.
“Kudirin kasafin kudi na 2024 ya mayar da hankali kan tsaro na cikin gida da sake farfado da tattalin arziki don magance hauhawar hauhawar farashin kayayyaki da barazanar talauci.
"Muna da yakinin kasafin zai dawo da yakinin 'yan Najeriya na samun shugabanni na-gari, la'akari da kasafin da aka gabatar a baya da ba su yi tasiri wajen ci gaban kasar ba."
- A cewar Olaniyi
SDP ta shirya goyon bayan gwamnatin Tinubu
Ya ce kasafin 2024 ya shafi wasu manyan bangarori da bukatun jama'a, inda ya kara da cewa idan har aka yi aiki tukuri, 'yan Najeriya za su yi farin ciki nan gaba kadan.
Olaniyi ya kuma shaidawa NAN cewa jam'iyyar SDP a shirye take ta goyi bayan gwamnatin Tinubu don kawo ci gaba ga Najeriya da zai sanya mutane farin ciki.
Kotun Koli ta yanke hukunci kan amfani da tsaffin kudi
A wani labarin, Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin Tinubu ta gabatar mata na kara wa'adin amfani da tsaffin takardun naira, Legit Hausa ta ruwaito.
A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, ta ce yanzu 'yan Najeriya za su iya ci gaba da amfani da tsaffi tare da sabbin kudin har illa-ma-shaa-Allah.
Asali: Legit.ng