Malamin Musulunci Ya Fadi Abin Da Zai Faru Idan Aka ‘Karbe’ Kujerar Gwamnan Kano

Malamin Musulunci Ya Fadi Abin Da Zai Faru Idan Aka ‘Karbe’ Kujerar Gwamnan Kano

  • Adam Abdallah Hotoro ya yi magana a kan zaben Kano da shari’ar da ake yi inda aka tsige gwamnatin NNPP
  • Shehin Malamin Addinin Musuluncin ya yi addu’a ga Allah SWT ya tabbatar da zabin da zai zama alheri a Kano
  • Sheikh Hotoro ya ce a tunaninsa, maslahar jihar Kano ita ce a bar mutane da wanda aka ba kuri’a lokacin zabe

Kano - Idan ana so al’ummar jihar Kano ta samu zaman lafiya, Sheikh Adam Abdallah Hotoro ya na ganin sai alkalan kotu sun yi adalci.

A wani bidiyon Tik Tok wanda aka wallafa a dandalin Facebook, an ji malamin addinin musuluncin ya na magana game da shari’ar Kano.

Shehin ya bada shawarar ayi adalci wajen sauraron shari’ar zaben Kano, yake cewa dole a damka hakki ga wanda ya mallaki wannan hakki.

Kara karanta wannan

Addu’ar nasarar APC a zaben Gwamnan Zamfara ta jawo Malami ya shiga uku

Gwamnan Kano
Kano: Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna Hoto: H.E Dr.Nasiru Yusuf Gawuna/Salisu Kosawa
Asali: Facebook

Kiran da aka yi kan shari'ar Gwmanan Kano

“Adalci shi ne ayi kokarin ba mai hakki hakkinsa, saboda shi ne zaman lafiya, cigaban al’umma da cigaban jihar Kano dinnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da yanzu ake shirin yi, Wallahi so ake yi sai an maida jihar Kano zamanin shekarun baya.
"Za mu samu kan mu cikin ci baya, kuma za a karya kimar Arewacin Najeriya.
"Ku rubuta ku ajiye, idan dai abin da ake shirin yi ya faru, bilLahil lazi la ila ha Illa Huwa, sai kun ce na fadi wannan magana."

Me zai faru idan aka tsige NNPP a Kano?

"Saboda za mu koma baya, bayan ma baya sosai. Za a cire kima da kwarjin mutane. Sannan da yawan mutane za su cire rai.
"Tun yanzu ka na ganin mutane da yawa su na cewa sun daina zabe, wasu su na fatan soja ya karbi kasar.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Yawan kuri'u ba shi ne kadai alamar nasara a zabe ba, cewar Doguwa

"Wasu mutane kuma su na kiran cewa juyin juya-hali ne ya dace da kasar. Wadannan duk ba su dace ba."

- Sheikh Adam Abdallah Hotoro

Shari'ar Kano: Menene abin da ya dace ayi?

Malamin ya bada shawara cewa abin da ya dace da masu tsoron Allah (SWT) shi ne su dage da zikiri da ambaton Allah domin ganin an yi adalci.

A jawabinsa, bai ambaci sunan kowane ‘dan siyasa ba illa ya roki abin da zai zama alheri tare da tunkude sharri ko da jama’a na matukar kaunarsa.

Amma malamin ya ce a fahimtarsa, zaman lafiya shi ne a bar 'Yan Kano da wanda su ka zaba, a cewarsa mai kokarin hawa mulki da karfi ya sani.

Zanga-zangar NNPP a Najeriya

Jagorori da magoya bayan jam’iyyar NNPP su na cigaba da zanga-zanga da addu’o’i a kan shari’ar Kano kamar yadda rahoto ya zo a baya.

Kara karanta wannan

Batun shari’ar zaben Kano ya yi girma, NNPP ta kai magana ECOWAS, EU da Amurka

An shirya zanga-zangar lumana a ofishin ECOWAS domin ankarar da duniya cewa karfa-karfa wajen tsige Gwamnan Kano zai jawo rigima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng