Wata Sabuwa: Jami'an tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zanga a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

Wata Sabuwa: Jami'an tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zanga a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka mamaye ofishin INEC da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi
  • Masu zanga-zangar waɗanda magoya bayan SDP ne sun mamaye ofishin INEC kan abin da suka kira kokarin sauya kayayyakin zabe
  • Sai dai tuni jami'an tsaron suka tarwatsa su da barkonon tsohuwa kana suka toshe titin zuwa ofishin INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon .shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Jami'an tsaro sun tarwatsa magoya bayan jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi waɗanda suka ɓarke da zanga-zanga a ofishin INEC da ke Lokoja.

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga.
Masu Zanga-Zanga Na SDP Sun Tarwatse Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye INEC a Kogi Hoto: Kogi State Map
Asali: UGC

Magoya bayan SDP sun mamaye babbar hedkwatar INEC da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi domin nuna adawa da abinda suka kira, "maguɗin takardun zaɓe."

Kara karanta wannan

Dino Melaye ya sha alwashin ba zai kallubalanci sakamakon zaben gwamnan Kogi ba, ya bada dalili

Da safiyar ranar Laraba, jami'an tsaron suka dira ofishin INEC domin daƙile duk wani yunkurin tada hargitsi a wurin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga isarsu wurin suka tarwatsa magoya bayan SDP da suka fito zanga-zanga ta hanyar harba barkonon tsohuwa mai sa hawaye, daga bisani suka toshe titin zuwa ofishin hukumar zaɓen.

Zanga-zangar ta fara cikin lumana kafin daga baya wasu daga cikin masu zangar-zangar da ke neman a kwashe kayan zaɓe a maida su Abuja, suka fara jifa da duwstsu.

Meyasa suka fito zanga-zanga?

Daya daga cikin masu zanga-zangar da ya bayyana sunansa da Danjuma ya ce suna da tabbacin cewa kayayyakin da ke ofishin hukumar zabe ta INEC, APC ce ta kirkire su.

A rahoton Vanguard, Mutumin ya ce:

"Muna da sahihin rahoto cewa APC da Yahaya Bello sun sauya kayayyakin zabe, waɗanda zasu ɗauka su kai kotun sauraron ƙararrakin zabe duk su suka tsara a abunsu."

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

"Saboda haka muka kira ga hukumar zaɓe ta gabatar da sahihan kayan zabe a gaban kotu ko kuma mu hargitsa jihar Kogi."

Takarar Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheka Daga ADC

A wani rahoton na daban Ɗan takarar mamban majalisar wakilan tarayya a inuwar ADC, Obinna Nwosu, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar.

A wata hira da Legit Hausa, Nwosu ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar ADC ne saboda mutanen mazaɓarsa sun roki ya sake lale.

Asali: Legit.ng

Online view pixel