Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Cikin Birnin Kano Kan Hukuncin Tsige Gwamna Abba

Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Cikin Birnin Kano Kan Hukuncin Tsige Gwamna Abba

  • Zanga-zanga ta kuma ballewa a jihar Kano ranar Laraba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna suna rera wakokin tir da hukuncin tsige Abba, a cewarsa Kano ta Abba ce
  • Mako biyu da suka gabata kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka wasu gungun masu zanga-zanga sun fantsama kan tituna a kwaryar birnin Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sabuwar zanga-zanga a Kano.
Zanga-Zanga Ta Kuma Ɓarkewa a Jihar Kano Kan Tsige Abba Gida-Gida Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Masu zanga-zangar a yau Laraba sun hau kan tituna suna nanata kalaman cewa, "Ba zamu yarda ba," "ba zamu bari ba" "Kano ta Abba ce," "Dole a kwato mana hakkin mu."

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Magoya bayan NNPP mata sun mamaye hedkwatar 'yan sanda a jihar Kano

Jami'an tsaro na ta kokarin tarwatsa su amma masu zanga-zangar sun dage, suna kara haɗuwa tawaga-tawaga su ci gaba da zanga-zanga, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda shari'ar zaben Kano ta gudana

Mako biyu da suka shige, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe karkashin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay, wanda ya tsige Gwamna Yusuf a watan Satumba.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta bayyana cewa kuri’u 165,663 na Yusuf, wanda ya tsaya takara a karkashin New Nigerian Peoples Party (NNPP), ba su da inganci.

Ta soke ƙuri'un bisa hujjar cewa basu ɗauke da sa hannu da hatimin hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC).

Daga nan sai kotun ta rage kuri’un gwamnan zuwa 853,939 yayin da Nasir Ganuwa, abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ke da ƙuri'u 890,705.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Mata sun barke da zanga-zanga a kan tsige Gwamnan Kano a Kotu

Gwamna Yusuf ya ki amincewa da hukuncin kotun, wanda ya bayyana a matsayin "rashin adalci" kana ya garzaya kotun daukaka kara, wadda ita ma ta yanke hukuncin tsige shi.

Bayan hukuncin ne, fargaba ta ƙaru a jihar Kano yayin da ƙungiyoyi suka rika sanya ranar gudanar da zanga-zanga amma jami'an tsaro suna hanawa saboda gudun tada tarzoma.

Haka nan kwana biyu da suka wuce watau ranar Litinin, mutane sun sake fitowa zanga-zanga amma daga bisani yan sanda suka tarwatsa su, rahoton Premium Times.

Gwamnan Jigawa ya yi magana kan matsalar tsaro

A wani rahoton kuma Gwamna Namadi na jihar Jigawa ya nuna damuwa kan yadda lamarin garkuwa da mutane ke karuwa duk mako a jihar.

Yayin da ya karɓi bakuncin sabon kwamishinan ƴan sandan Jigawa, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba zata lamurci lalacewar tsaron a'umma ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262