Masu Zanga-zanga Sun Kai Hari Kan Sojoji Yayin Nuna Rashin Jin Dadi Kan Hukuncin Zaben Gwamnan APC
- Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a jihar Nasarawa kan hukuncin kotu, rundunar soji ta yi martani kan harin da aka kai musu
- Rundunar ta yi Allah wadai da harin da masu zanga-zangar su ka kai wa ayarin motocinsu a kan hanyar Lafia zuwa Makurdi
- Masu zanga-zangar daga bisani sun zargi rundunar sojojin da kai musu hari yayin da su ke tsaka da nuna bacin ransu kan hukuncin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Nasarawa - Rundunar sojin Najeriya ta yi Allah wadai da harin da masu zanga-zanga su ka kai musu a jihar Nasarawa.
Masu zanga-zangar na muna damuwarsu ce kan hukuncin kotun daukaka kara da aka yanke a zaben gwamnan jihar.
Mene ya faru yayin zanga-zangar a Nasarawa?
Matasan sun tare hanyar Lafia zuwa Makurdi inda su ka kai hari kan ayarin motocin rundunar da ke wucewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai na rundunar, Janar Onyema Nwachukwu shi ya bayyana haka a shafin Twitter na rundunar.
Onyema ya ce wannan abin Allah wadai ne yadda mutanen su ka farmaki ayarin motocinsu da ke wucewa a hanyar.
Wane martani rundunar ta yi?
Ya ce:
"Mu na Allah wadai da wannan lamari na masu zanga-zangar da su ka zabi tare hanya.
"Wannan mataki ya na jawo hargitsi a kan hanya tare da hana mutane masu wucewa yayin da su ka farmaki motocin rundunarmu.
"Abin takaici shi ne yadda masu zanga-zangar su ka yi sharrin cewa motocin rundunarmu ne su ka nemi murkushe su."
Onyema ya ce akwai hujjoji na faifan bidiyo da hotuna da ke nuna yadda rundunar ta ke kokarin korar masu zanga-zangar cikin hikima, cewar Vanguard.
Ya ce rundunarsu ta na kare martabar mutane da kuma hakkokinsu inda dole mutane su na gudanar da zanga-zanga kamar yadda doka ta tanadar.
Kotu ta yi hukunci kan zaben Nasarawa
A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule Abdullahi na jihar Nasarawa wanda ke jami'yyar PDP.
Har ila yau, kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu saboda rashin hujjoji.
Asali: Legit.ng