Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

  • Dino Malaye ya kammala karatun digirin digirgir bayan shekaru da cece-kucen da ya faru akansa
  • A baya an taba zargin Dino Malaye da ba da takardar kammala karatu ta bogi daga jami'ar Ahmadu Bello
  • Gashi Dino Malaye a wannan karo ya shaidawa duniya cewa, ya kammala karatunsa na digiri na biyu

Dino Melaye, tsohon sanata wanda ya wakilci gundumar sanata amajalisar kasa ta takwas, ya kammala karatun digiri na biyu a kan nazarin manufofi daga Jami'ar Abuja.

Tsohon dan majalisar ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Laraba da yamma, 14 ga Yuli, don nuna murnar sabuwar nasarar da ya samu.

KARANTA WANNAN: Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Shekaru bayan da aka zargi Dino Malaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu
Dino Melyaye | Hoto: dailypost.ng
Asali: Instagram

Melaye wanda abokin hamayyarsa na siyasa, Smart Adeyemi ya tsayar da kudirinsa na komawa majalisar dattijai ta tara, ya nuna kwafin sakamakon kammala karatun da jami'ar tarayya ta ba shi tare da taken:

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

"Daukaka ta tabbata ga Allah har abada."

Legit.ng ta lura cewa sakamakon kammalawar mai dauke da kwanan watar 26 ga watan Nuwamba 2019 ta samu sa hannun mataimakin mai rajistara na jami'ar, Alkasim M. Umar.

Bayanin sakamakon ya karanta sashi:

"Wannan shi ne tabbatacin cewa Melaye Dino Daniel mai lambar rajista 09493211 bayan ya kammala karatun da aka amince da shi, kuma ya ci jarabawar da aka tsara, a karkashin ikon Majalisar Dattawa, an ba shi M.Sc. Policy Analysis."

Dubun-dubatar ‘yan Najeriya sun mayar da martani game da rubutun tsohon sanatan a shafin Facebook.

Ben C Odai ya ce:

"Ina taya ka murna Dino.
"Idan bukatar hakan ta taso, inda aka nemi ka gabatar da sakamakonka don tabbatarwa, da farin ciki za ka gabatar da shi kuma ka sanar da shi kamar yadda ka yi yanzu, ba tare da daukar SANs 14 da Lauyoyi 10 zuwa kare sakamakonka a Kotun Koli ba."

Kara karanta wannan

Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado

Maria Chukwudozie ta ce:

"Kai Oga Dino ta yaya ka samo irin wannan sakamakon. Ba ka taba zuwa makaranta ba na kwana ɗaya kuma yanzu an ba ka takardar shaidar M.sc. Hmmmmm Najeriya kasarmu."

Isaac Ediba ya ce:

"Kwararren bujumi na ilimi, dan gwagwarmayar zamantakewar al'umma, baya gajiya da kara darajar rayuwarsa duk da nasarorin da ya samu. Ina taya murna yallabai."

Dino Melaye ya caccaki Ndume kan badakalar takardar kammala karatu

Legit.ng a baya ta ruwaito cewa a shekarar 2017, Sanata Melaye ya caccaki Sanata Ali Ndume kan neman majalisar dattijai da tayi bincike kan zargin cewa bai kammala karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ba.

Melaye ya shiga cikin rikici a lokacin bayan da rahotanni daga Sahara Reporters suka nuna cewa duk da cewa ya halarci ABU, amma bai kammala karatun ba.

Ndume ya kasance a zauren majalisar a ranar Talata, 20 ga Maris, 2017, yayin da ya gabatar da wata bukata inda ya nemi Majalisar Dattawa ta binciki zargin.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

KARANTA WANNAN: Korona: Gwamnati ta gargadi Musulman Najeriya game da yawon sallah da zuwa Idi

Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

A wani labarin, A yammacin jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokoki ta kasa, domin gudanar da wata liyafa.

Shugaban kasar ya tattauna da 'yan majalisu da sanatocin, yayin da ya bayyana wasu maganganu ciki har da yabo da ba da tabbaci da goyon baya a gwamnatinsa.

Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, inda ya nemi goyon baya wajen magance su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel