Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Babban Mukami a Gwamnatinsa, An Bayyana Sunansa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada muhimmin mukami a gwamnatinsa a yau Litinin
- Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma'a'ikatan gidan gwamnati, Alhaji Abdullahi Musa
- Wannan na zuwa ne bayan murabus na tsohon shugaban ma'aikatan, Alhaji Usman Bala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nada sabon shugaban ma'a'ikatan gwamnatin jihar.
Abba ya nada Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma'a'ikatan wanda zai fara aiki nan take, cewar TVC News.
Mene dalillin nada sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin?
Wannan na zuwa ne bayan murabus din tsohon shugaban ma'aikatan, Alhaji Usman Bala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Kabir ya ci gaba da tafiya da Usman Bala tun bayan hawanshi mulki a watan Mayun wannan shekara.
Sabon shugaban ma'a'ikatan, Musa ya fito daga karamar hukumar Kiru da ke jihar, cewar Daily Trust.
Wanene sabon shugaban ma'aikatan gwamnatin?
Ya shafe fiye da shekaru 30 ya na aikin gwamnati a bangarori da dama na gwamnati.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Litinin 27 ga watan Nuwamba.
Dawakin Tofa ya ce sabon shugaban ma’aikatan gogaggen ma’aikacin gwamnati ne wanda ya ke da kwarewa a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin Kano daban-daban.
Musa ya kammala digiri dinsa na farko a fannin nazarin harkokin diflomasiyya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Har ila yau, ya kammala digiri na biyu a fannin tsare-tsare da gudanarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Tsohon gwamna ya fadi abin da ke faranta masa rai
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano a mulkin soja, Kanal Sani Bello ya bayyana abin da ke faranta masa rai a rayuwarsa.
Kanal Bello ya ce ganin farin ciki a fuskar marasa karfi ke sanya ma sa ni'ima a rayuwarsa.
Ya ce duk lokacin da yaga marar lafiya ya samu sauki dalilin Gidauniyarsu abin na faranta ma sa rai.
Asali: Legit.ng