Gwamna a Najeriya Ya Watsar da Katafaren Gidan Gwamnati, Ya Na Gudanar da Gwamnatinsa Daga Kauyensu

Gwamna a Najeriya Ya Watsar da Katafaren Gidan Gwamnati, Ya Na Gudanar da Gwamnatinsa Daga Kauyensu

  • Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi abin mamaki yayin da ya ke gudanar da gwamnati daga wani kauye a jihar
  • An tabbatar da cewa Otti na gudanar da gwamnatinsa a kauyen Umuru Umuehi a karamar hukumar Nvosi, Isiala-Ngwa ta Kudu
  • Kakakin gwamnan, Kazie Uko ya tabbatar da cewa Otti ba ya gudanar da gwamnati daga sabo da kuma tsohon gidan gwamnatin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia – Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya watsar da sabon gidan gwamnatin jihar na biliyoyin nairori tun bayan hawanshi mulki a watan Mayu.

Otti na gudanar da harkokin gwamnatin jihar a kauyen Umuru Umuehi a karamar hukumar Nvosi, Isiala-Ngwa ta Kudu da ke jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da gwamnoni uku, ya musu nasihar yadda zasu ɗauki talakawa

Gwamna Alex Otti na jihar Abia na gudanar da gwamnatinsa daga kauyensu
Gwamnan ya bayyana dalilin barinsa gidan gwamnatin. Hoto: @alexottiofr.
Asali: Facebook

Tun yaushe Otti ya bar gidan gwamnatin?

Premium Times ta tattaro cewa tsohon gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu ya kammadar da sabon gidan gwamnatin kwana daya kafin Otti ya hau mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Otti tun bayan hawanshi mulki ya bar gidan inda ya ke gudanar da gwamnatinsa daga kauye.

Har ila yau, rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan ba ya amfani da tsohon gidan gwamnatin da aka bar amfani da shi.

Wane martani gwamnatin Otti ta yi?

An baza jami’an tsaro a kauyen Umuru Umuehi don gadin gidan da Gwamna Otti ya ke zaune a kauyen, Legit ta tattaro.

Kakakin gwamnan, Kazie Uko ya tabbatar da cewa Otti ba ya gudanar da gwamnati daga sabo da kuma tsohon gidan gwamnatin.

Uko ya ce Otti ba ya amfani da shi ne saboda wadanda su ka bar gidan gwamnatin sun kwashe dukkan kayan da ke ciki.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da ake rudanin shari'ar zabe, Abba Kabir ya sallami ma'akata dubu 3, ya bayyana dalili

Dillalan shanu daga Arewa sun nemi taimako

A wani labarin, dillalan shanu ‘yan asalin Arewacin Najeriya sun roki Shugaba Tinubu da ya kawo musu dauki bayan sanarwar tayar da su a kasuwa.

‘Yan kasuwar sun mika rokon ne yayin da Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ba su wa’adin makwanni biyu don tashi daga kasuwar.

Wannan na zuwa ne bayan zargin su na boye 'yan ta'adda a cikin kasuwar shanun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.