Matawalle v Dauda: Rikicin Siyasa Ya Sa Limamin Juma’a Ya Bar Masallaci a Zamfara
- Babban malamin nan, Tukur Sani Jangebe ya sauka daga matsayinsa na yin limanci a masallacin Juma’a a jihar Zamfara
- Limamin ya bar kujerarsa ne saboda a samu zaman lafiya a masallacin kamar yadda ya sanar a wasikar yin murabus dinsa
- Rigimar siyasar da ke tsakanin Bello Matawalle da sabon Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare ya shafi Sheikh Jangebe
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Zamfara - A sakamakon irin sabanin da ke tsakanin Bello Matawalle da magajinsa, Dauda Lawal Dare, limami ya sauka daga matsayinsa.
Punch ta ce rigimar siyasar jihar Zamfara ta yi sanadiyyar da babban limamin wani masallaci a GRA, Sheikh Tukur Sani Jangebe ya sauka.
Tsohon Kwamishinan addinin Zamfara
Sheikh Tukur Sani Jangebe ya aika wasika zuwa ga shugaban masallacin da yake limanci, ya sanar da su ya hakura daga limancin Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Limamin wanda ya taba rike kujerar Kwamishinan addinai ya ce ya yi hakan ne saboda tabbatar da zaman lafiyar masallacin da al’umma.
Duk da haka, Tukur Sani Jangebe ya bayyana cewa a shirye yake, ya bada duk wani gudumuwa wajen cigaban masallacin, musulunci da jihar.
Zamfara: Wasikar Tukur Sani Jangebe
“Na rubuta takardar nan domin sanar da ku niyyata na yin murabus a matsayin babban limamin masallacin Juma’an GRA daga 23 ga Nuwamba 2023.
Abin takaici, na dauki matakin nan ne saboda kwadayina na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma aminci a masallacin.
Ina so in nuna matukar godiya ga damar da aka ba ni na zama cikin jagororin masallacin wanda ya ba ni damar shugabantar masallacin a matsayina.
- Sheikh Tukur Sani Jangebe
Rikicin siyasar jihar Zamfara
Rahoton ya ce babban malamin ya samu kan shi a tsaka mai wuya ne bayan fitowar wani bidiyo inda aka ji ya na yabon gwamnatin Bello Matawalle.
Gwamna Dauda Lawal Dare da ake zargin limamin ya kushe, shi ya gyara masallacin da malamin yake limanci a unguwar GRA da ke jihar Zamfara.
Shari’ar zaben Gwamnan jihar Kano
Ana da labari cewa wadanda su ka niyyar fita zanga-zanga a Kano ba su iya ba saboda an baza jami’an tsaro domin hana tashin hankali a jihar.
Magoya bayan jam’iyyun NNPP da APC masu shirin yin salloli, addu’o’i, zanga-zangar lumana da kuma taron murna sun hakura saboda matakan tsaro.
Asali: Legit.ng