Rikicin Rivers: Gwamna Fubara Ya Sake Kalubalantar Nyesom Wike
- Rikicin siyasar jihar Rivers ya ɗauki sabon salo yayin da gwamna Fubara ke kare tushensa na ƙabilar Ijaw
- Yayin da Wike ya dage cewa ya ƙyamaci masu butulci, Fubara ya ce shi mutum ne tsayayye wanda ya fito daga Ijaw kuma ba ya tsoron ƙalubale
- Ana dai cigaba da fafatawa a tsakanin ƴan siyasan biyu inda su ke cigaba da cacar baki a bainar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Rikicin da ake ganin ya ɓarke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da kuma magabacinsa, Nyesom Wike ya ɗauki wani sabon salo inda dukkansu biyun suka riƙa sukar juna.
Fubara ya ce wadanda suka cire ƴan ƙabilarsa na Opobo daga zama ƴan ƙabilar Ijaw ba su da tarihin yankin Neja Delta.
PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya yi watsi da wasu kalamai na cewa shi ba ɗan ƙabilar Ijaw bane a lokacin da ya gana da wakilan Kalabari Se Kobiri a gidan gwamnati dake Port Harcourt a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan da ministan babban birnin tarayya Abuja, Wike, a yayin da yake magana kan rikicin jihar, ya ce kuɗi da mulki na bayyana haƙiƙanin mutum, cewar jaridar Vanguard.
Gwamna Fubara ya yabi tsatsonsa
A cewar Fubara, ƴan ƙabilar Ijaw mutane ne masu jajircewa, waɗanda duk da cin mutuncin da aka yi musu, ba su bari an siyar da su ba a lokacin cinikin bayi.
Ya nanata cewa yana da imani guda ɗaya, wato nufin Allah ne kaɗai ke yin galaba a kowane yanayi, mai kyau ko mara kyau, nasara ko kasawa.
Akwai Matsala: Yan majalisa 27 cikin 31 sun juya wa gwamnan PDP baya yayin da ake yunkurin tsige shi
A kalamansa:
"Domin haka duk wanda ke ba ku wannan bayanin, to ya koma ya binciki tarihi. Ba za a iya magana game da gwagwarmayar Ijaw ba tare da Opobo, Bonny, da Kalabari ba."
"Muna da layukan kasuwancin mu a wancan lokacin, sannan idan ka samu layin kasuwanci, hakan na nufin kai cikakken ɗan ƙabilar Ijaw ne. Saboda haka ni cikakken ɗan ƙabilar Ijaw ne daga jini har zuwa ƙasusuwa na."
Gwamna Fubara Ya Saduda a Rikicinsa da Wike
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya saduda kan rikicin siyasar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
Gwamna Fubara a yayin wani taro ya bayyana cewa ministan na birnin tarayya Abuja zai cigaba da zama shugabansa.
Asali: Legit.ng