Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ke Neman Tsige Gwamnan PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ke Neman Tsige Gwamnan PDP

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom
  • Kotun ta tabbatar gwamnan na jam'iyyar PDP a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar
  • A hukuncin da kotun ta yanke ta yi nuni da cewa ƙarar da masu ɗaukaka ƙarar suka shigar ba ta cancanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Legas ta yi watsi da ƙarar da neman soke zaɓen Gwamna Umo Eno na jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom.

Sanata Bassey Albert Akpan da jam’iyyarsa ta Young Progressives Party tare da Akanimo Udofia na jam’iyyar APC da Sanata John Akpanudoedehe na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ne suka shigar da ƙarar, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan APC

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno
Kotun daukaka ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom Hoto: Pastor Umo Eno
Asali: Twitter

A wasu hukunce-hukunce daban-daban da aka yanke ranar Juma’a a Legas, Kotun ɗaukaka ƙara ta yi fatali da ƙararrakin da masu ɗaukaka ƙara ukun suka yi, inda ta bayyana su a matsayin marasa cancanta, rahoton The Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotu ta yi fatali da ƙararrakin?

Kotun ta yanke hukuncin cewa waɗanda suka shigar da ƙara sun rasa wannan batu ne inda suka ce tunda ba su cikin ƙarar, hukuncin da aka yanke kan batun satifiket ɗin bai hau kansu ba.

"Hukuncin da kotun da ke da ikon yanke hukunci ta yanke, hukunci ne da ya shafi duniya baki daya, ba wai kawai waɗanda ke cikin shari’ar ba." A cewar kotun.

Kotun ta yi Allah wadai da cin mutuncin kotu da masu ɗaukaka ƙarar suka yi ta hanyar sake shigar da ƙara kan batun da babbar kotu, kotun ɗaukaka ƙara da kotun ƙoli suka yanke wanda ya ba Umo Eno nasara.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 na sani yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci kan soke zaben gwamnan Nasarawa

Da ta ke yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar YPP ya shigar, kotun daukaka kara ta kuma nuna rashin jin dadinta kan gazawar masu shigar da ƙara wajen kiran shaidun da suka halarci zaɓukan a matsayin wakilan zaɓe, don tabbatar da magudin zaɓe.

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Caccaki INEC

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta caccaki hukumar zaɓe ta INEC bisa goyon jam'iyyar siyasa a shari'ar zaɓe.

Kotun ta gargaɗi INEC kan goyon bayan wata jam'iyya a kotu inda ta ce kamata ya yi hukumar ta ɗauki matsayin tsaya wa tsaka tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng