Wike Ya Caccaki Gwamna Fubara, Ya Bayyana Wani Babban Laifi 1 da Ya Yi Daga Hawansa Mulki
- Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicin siyasar da ke tsakaninsa da Gwamna Fubara na jihar Rivers
- Wike ya bayyana Fubara a matsayin butulu wanda bayan hawansa mulkin jihar ya kawo rikici a cikinta
- Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi nuni da cewa ya yi abubuwa da dama domin ganin gwamnan ya ji daɗin mulkinsa amma sai ya yi masa butulci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, inda ya bayyana shi a matsayin butulu.
Wike, tsohon gwamnan Rivers, ya bayyana hakan ne lokacin da ya yi hira da wasu zaɓaɓɓun ƴan jarida a ranar Juma'a kan rikicinsa da Gwamna Fubara, cewar rahoton Daily Trust.
Akwai Matsala: Yan majalisa 27 cikin 31 sun juya wa gwamnan PDP baya yayin da ake yunkurin tsige shi
Dangantaka tsakanin Wike da Fubara ta yi tsami ne ƙasa da watanni shida da miƙa mulki a hannun gwamnan na jihar Rivers.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin dai ya yi ƙamari ne makonnin da suka gabata inda aka ƙona zauren majalisar dokokin jihar da kuma yunƙurin tsige gwamnan.
Wike ya caccaki Gwamna Fubara
Da yake magana kan rikicin da ya addabi jihar, Wike ya bayyana cewa baya son mutane masu butulci.
A kalamansa:
"Bari in gaya muku, ba na son butulu, ba zan iya jurewa ba. Abin da ke faruwa a yanzu shi ne abin da Odili ya ce a cikin littafinsa: 'Ka ba wa mutum mulki da kuɗi, sannan za ka san mutumin."
"Idan ba ka ba mutum, mulki da kuɗi ba, to ba ka san mutumin ba. Duk da haka, ban damu ba saboda ni ɗan siyasa ne. Na san abin da wasu jihohi ke fama da su saboda bashi, amma ku je ku duba ko na bar bashi, bayanan suna nan."
“Na bar masa ayyuka ya ƙaddamar da su domin ya baje koli a cikin kwanakinsa ɗari, sai siyasa ta shigo, yanzu muka fara. Allah ya baka wani abu, yanzu kuma kana shigo da rikici."
"Allah ya ba ka wannan abun a sauƙaƙe, gwamnatin tarayya ba ta yaƙar ka, babu rikici, amma kai ne yanzu ke kawo wa kanka rikici. Waɗanda dama butulu ne kawai za su goyi bayan abin da ke faruwa. Ina amfani da doka domin yaƙi ba ƴan daba ba, lokaci zai zo."
Gwamna Fubara Ya Saduda a Rikicinsa da Wike
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya saduda kan rikicin siyasar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
Gwamna Fubara a yayin wani taro ya bayyana cewa ministan na birnin tarayya Abuja zai cigaba da zama shugabansa
Asali: Legit.ng