PDP Ta Kara Shiga Matsala Yayin da Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Yan Majalisa 11 a Jihar Filato
- Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori ‘yan majalisa 11 na jam’iyyar PDP a Filato
- Kotun daukaka kara ta kori yan majalisar PDP 11 a majalisar dokokin jihar Filato a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba
- Kwamitin da Mai Shari’a Okon Abang ya jagoranta ya yanke hukuncin cewa PDP ba za ta iya daukar nauyin ‘yan takara a zaben da ya gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta tsige yan majalisa 11 na jam'iyyar PDP a majalisar dokokin jihar Filato a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.
A wani hukunci na bai daya, kwamitin kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Okon Abang, ya tabbatar da cewar dukkan yan majalisar da aka tsige sun samu kuri'u marasa amfani a zabenna watan Maris saboda jam'iyyarsu bata da tsari, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya kara da cewar jam'iyyar PDP ta saba sashi na 177 na kundin tsarin mulkin 1999, saboda haka ba za ta iya daukar nauyin yan takara a zabe ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda haka, kotun ta ayyana dukkanin wadanda suka zo na biyu a zaben na ranar 18 ga watan Maris a matsayin wadanda suka lashe zabe.
Jerin yan majalisar da kotu ta tsige
- Hon Timothy Dantong (Riyom)
- Hon. Rimyat Nanbol,- (Langtang ta Arewa ta Tsakiya)
- Moses Sule (Mikang)
- Salome Waklek,-(Pankshin)
- Hon. Bala Fwangji (Mangu ta Kudu)
- Hon. Maren Ishaku (Bokkos)
- Hon. Dagogot (Quaanpan ta Arewa)
- Hon Nannim Langyi,-(Langtang ta Arewa maso Arewa)
- Hon Nimchak Rims (Langtang ta Kudu)
- Hon. Danjuma Azi (Jos ta Arewa maso Yamma)
- Hon Gwottson Fom (Jos ta Kudu)
- Hon. Abubakar Sani idris (Mangu ta Arewa)
A yanzu jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ce jam'iyya mai jagoranci a majalisar.
Kotu ta tabbatar da zaben Nasir Idris
A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta tabbatar da nasarar Nasir Idris a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar Kebbi a zaben ranar 18, ga watan Maris.
Kwamitin kotun mai mutum uku, ya bayyana a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, cewa karar da jam'iyyar PDP da dan takararta na zaben gwamnan, Janar Aminu Bandel bai da inganci, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng