Wike Ya Magantu Kan Yiwuwar Karawa Da Tinubu a Zaben 2027
- Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi karin haske cewa ba zai yi takarar shugaban kasa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a 2027
- Da yake magana a wani shirin kai tsaye na gidan talbijin wanda Legit Hausa ta bibiya, Wike ya ce shi dan halas ne
- A yayin hirar, Wike ya jaddada jajircewarsa don ganin gwamnatin Tinubu ta yi nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce shi dan amana ne kuma ba zai kara da Shugaban kasa Bola Tinubu ba a zaben 20217.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hirar kafar watsa labarai a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, wanda Legit Hausa ta bibiya.
Wike ya yi mubaya'a ga Tinubu
Kamar yadda ya bayyana, babu abun da zai shafi biyayyarsa ga shugaban kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalamansa:
"Tinubu ya nada ni minista, mutane basu fahimta ba, Ni dan halas ne. Me zai faru a 2027? Na tsaya sannan na ce ba an goyi bayan rashin adalci ba.
"An yi mun barazana cewa za yi mun wannan za su yi mun wancan. Sun gwada matakai da dama ciki harda amfani da manyan Janarori."
Kalli bidiyon hirar Wike a kasa wanda tashar AIT ta daura.
Ministan ya kara da cewar kasancewar ya yi aiki wajen bayyanar Tinubu a matsayin shugaban kasa kuma sannan aka nada shi ministan Abuja, toh babu abun da zai sa shi karawa da shugaban kasar a 2027.
APC ta bar Wike yana cin karensa
A wani labarin, mun ji cewa Rotimi Amaechi ya sake cin karo da cikas a tafiyar siyasa inda shugabannin APC na kasa su ka sauke shugabanninta na reshen Ribas.
Rahoton Daily Trust ya ce an yi waje da mutanen Rotimi Amaechi daga jam’iyyar APC, an kawo sababbin shugabannin rikon kwarya a jihar Ribas.
Shugabannin rikon kwaryan da aka nada mutanen Nyesom Wike wanda yanzu haka shi ne Ministan harkokin Abuja, kuma jigo a jam’iyyar PDP.
Shekaru kusan goma kenan ana rigimar siyasa tsakanin Nyesom Wike da tsohon ubangidansa watau Amaechi wanda ya yi minista kafinsa.
Asali: Legit.ng