'Yan Bindiga Sun Bindige Shugaban PDP Har Lahira a Gaban Idon Matarsa, an Fadi Wacce Ake Zargi

'Yan Bindiga Sun Bindige Shugaban PDP Har Lahira a Gaban Idon Matarsa, an Fadi Wacce Ake Zargi

  • 'Yan bindiga sun bindige wani shugaban jam'iyyar PDP a karamar hukumar Ezinihitte Mbaise da ke jihar Imo
  • Smith Chiedoziem shi ne shugaban PDP a yankin Ife/Akpodim/Chokoneze da ke karamar hukumar Ezinihitte Mbaise
  • Wannan na zuwa ne bayan jami'yyar PDP ta sha kaye a zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin shugaban jam'iyyar PDP, Smith Chiedoziem Anyanwu a jihar Imo.

Marigayin shi ne shugaban jam'iyyar PDP a yankin Ife/Akpodim/Chokoneze da ke karamar hukumar Ezinihitte Mbaise a jihar, Vanguard ta tattaro.

Mahara sun bindige shugaban jam'iyyar PDP a jihar Imo
'Yan bindiga sun yi ajalin shugaban PDP a jihar Imo. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Twitter

Yaushe shugaban PDP ya rasu a Imo?

Smith ya rasa ransa ne a jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamba yayin da mahara su ka je har gidansa su ka bindige shi.

Kara karanta wannan

Ganduje ya saka lalubule da tsohon shugaban kasa a gidansa da ke Abuja, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan jami'yyar PDP a bangaren yada labarai, Lancelot Obiaku shi ya bayyana haka a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba a Owerri.

Obiaku ya ce:

"Tabbas wannan mummunan lamari ya faru."

Sai dai Obiaku bai yi karin bayani kan kisan Smith ba wanda ya mutu a jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

Sai dai wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun hallaka Smith a gaban idon matarsa inda ya ce sun zo ne a kan babura.

Ya ce:

"Yan bindigan sun hallaka shi ne a gaban idon matarsa kafin daga bisani su tsere a kan babura.
"Maharan su biyu ne inda su ka tambayi inda mijin matar ya ke, can sai su ka hango shi inda su ka harbe shi sai da su ka tabbatar ya cika.

Majiyar ta ce akwai wata mata da ta yi bazaranar illata shi yayin da ake gudanar da zaben gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Wannan na zuwa ne bayan jami'yyar ta sha kaye a zaben da aka gudanar a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba, Daily Post ta tattaro.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Henry Okoye bai yi karin haske ba kan lamarin.

Samanja mazan fama ya rasu

A wani labarin, Shahararren dan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi ya riga mu gidan gaskiya.

Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama ya rasu a gidansa da ke birnin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.