Kungiyar Duniya Ta Fusata da Cafke Masu Zanga Zanga a Kano Saboda Tsige Abba

Kungiyar Duniya Ta Fusata da Cafke Masu Zanga Zanga a Kano Saboda Tsige Abba

  • Amnesty International ta goyi bayan wadanda su ka fito zanga-zanga saboda rashin gamsuwa da hukuncin shari’ar zaben Kano
  • Kungiyar ta fitar da jawabi cewa mutane suna da hakkin gudanar da zanga-zangar lumuna, hakan bai sabawa dokar kasa ba
  • Bayan kyale matasan da ke hannun ’yan sanda, Amnesty International ta bukaci a danke duk jami’an tsaron da su ka yi ram da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Kungiyar Amnesty International mai kare hakkin Bil Adama a duniya ta yi magana a kan cafke masu zanga-zanga a jihar Kano.

A sakamakon tsige gwamna Abba Kabir Yusuf da kotun daukaka kara tayi a makon jiya, wasu sun yi zanga-zanga domin nuna fushinsu.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano tare da 'yan sanda Hoto:Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Zanga-zanga a Kano: Amnesty International tayi Allah wadai

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir, APC sun ja layi kan zanga-zangar da aka gudanar bayan fitar da takardun CTC

Daily Nigerian ta rahoto Amnesty International ta na tir da matakin da ‘yan sanda su ka dauka na cafke wadanda su ka hau kan tituna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an tsaro sun fatattaki jama’a har ta kai an yi ram da mutane bakwai da aka kama.

A jawabin da Amnesty International ta fitar a ranar Alhamis, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta binciki abin da ya faru kuma a dauki mataki.

Kungiyar ta na so a hukunta jami’an tsaron da suka yi wannan aiki,sannan a gaggauta sakin mutanen da ke tsare saboda zanga-zangar.

Kano: Jawabin Kungiyar Amnesty Int'l

"Ba tare da wani sharadi ba, dole ayi gaggawar sakin mutane bakwai da ke zanga-zanga da ‘yan sanda su ka kama.
Mutanen Kano su na da cikakkiyar dama gudanar da zanga-zanga.
Karfa-karfan da aka yi jiya (Laraba) karara ya nuna cewa hanyar yi wa mutane barazana ne a hana su ‘yancinsu.

Kara karanta wannan

Kano: ‘Yan sanda sun cafke mutanen da ke zanga zanga saboda kotu ta tsige Abba

‘Yan sanda sun rika fesa borkonon tsohuwa da ruwa domin a fatattaki masu zanga-zanga, aka yi wa da-dama rauni.
Wajibi ne hukumomin Najeriya su kama wadanda ake zargi da danne hakkin Kanawan da su ka fita zanga-zanga
Sannan a hukunta su a kan laifuffukansu kuma a tabbatar da yi wa ‘yan zanga-zangan adalci."

- Amnesty International

CTC sun jawo rikici a Kano wajen tsige Abba

Rahoto ya zo cewa kotun koli kurum za ta iya raba gardama tsakanin NNPP da APC a shari'ar zaben Kano bayan rikici a kan takardun CTC.

Lauyan NNPP, Wole Olanipekun SAN ya ce a kaddara a takardar hukuncin akwai wasu kura-kurai, lokaci ya kure da za ayi wani gyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng