Gwamna Ya Sa Labule da Ganduje Jim Kadan da Samun Nasarar APC a Shari’ar Zabe
- Gwamnan jihar Nasarawa ya zauna da Abdullahi Umar Ganduje da kotu ta ba shi nasara a shari’ar zaben Gwamnan 2023
- Abdullahi Sule da sauran tsofaffin Gwamnonin jihar Nasarawa sun kai wa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ziyara a Abuja
- Ana tunanin jagororin jam’iyyar ta APC sun yaba da rawar da Ganduje ya taka wajen karbe nasarar da aka fara ba PDP
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya dauki tawagar jagororin jam’iyyar APC zuwa wajen Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Punch ta ce Mai girma Abdullahi Sule ya ziyarci shugaban APC na kasar ne bayan nasarar da ya samu a kotun daukaka kara a ranar Alhamis.
Dr. Ganduje ya hadu da Gwamnan Nasarawa
Alkalai sun tabbatar da cewa Sule ya lashe zaben gwamnan Nasarawa, wannan ya rusa hukuncin farko da kotun sauraron karar zabe ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda gwamnan mai-ci ya dauka sun hada da magabatansa kuma jagororin APC; Abdullahi Adamu da Umar Tanko Al-Makura.
Legit ta na tunanin wannan ne karo na biyu da Sanata Abdullahi Adamu ya hadu da magajinsa a APC NWC watau Dr. Abdullahi Ganduje.
Meya kai Gwamna Sule wajen Ganduje?
An yi zaman ne a bayan labule, saboda haka rahotonni ba su bayyana abin da aka tattauna ba, sai daga baya ne hotuna su ka fara yawo.
Ana tunanin Gwamna Sule da mutanensa sun je Abuja ne domin yi wa Abdullahi Ganduje godiya saboda gudumuwar da ya ba ba jam’iyyar.
Mutane sun fara jefa tambayoyi ga APC
Sai dai a matsayinsa na shugaban APC na kasa, jama’a suna kokawa da cewa doka da tsarin mulki ba su ba Ganduje wata dama a kotu ba.
A yanzu Ganduje ne yake juya akalar kotuna?
- Hamma Hayatu
Shi kuma wani masoyin Atiku Abubakar mai suna Abdullahi Abdullatif, ya yi kira ne Dr. Abdullahi Ganduje ya ji tsoron Allah (SWT).
"Ganduje ka ji tsoran ranar da za ka tsaya a gaban Ubangijinmu tsirara, ka da abin ya ki maka kyau domin babu gyara a wannan lokacin fa."
- Abdullahi Abdullatif
Shi kuwa Malam Muhammad Gambo Ibrahim tambaya yake yi ko shugaban na APC ya zama shugaban bangaren shari’a a Najeriya ne.
Hukuncin zaben Gwamnan Kano
Ana da labari Farfesa Chidi Odinakalu yana ta cigaba da bankado bayanai game da tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana ganin akwai lauje a nadi.
Masanin shari’ar ya ce cikin Alkalan da su ka tsige Gwamnan Kano, su ka ba APC nasara akwai 'dan Alkalin Alkalai wanda aka nada a shekarar nan.
Asali: Legit.ng