Kuskuren Cikin Takardun Hukuncin Kano Ba Tuntuben Alkalami ba ne Inji Farfesa Odinkalu
- Farfesa Chidi Odinkalu ya na daga cikin masu ganin ba kuskure kotu ta yi a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano ba
- Masanin shari’ar ya ce abin da ya faru ya fi karfin a kira shi da tuntuben alkalami daga alkalai ko akawun kotu
- Chidi Odinkalu ya fadawa duniya cewa kotun daukaka kara ba za ta iya yin tafka da warwara kuma ta gyara yanzu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Chidi Odinkalu ya yi karin haske game da bayanai masu cin karo da juna da aka samu a takardun hukuncin shari’ar gwamnan Kano.
Farfesa Chidi Odinkalu ya zanta da tashar Channels TV a ranar Laraba, ya nuna sam bai yarda a ce tuntuben alkalami aka samu daga kotu ba.
A wasu wuraren, bayanan da aka fitar a takardun CTC da farko sun nuna NNPP ce ta samu nasara a kotu, masanin shari’ar ya ce da walakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CTC: Ana gyara kuskure a kotu?
Farfesa Odinkalu ya ce akwai dokar tuntube a kotu wanda ake amfani da ita wajen gyara kananan kura-kurai da aka yi wajen rubuta hukunci.
Amma ganin yadda aka rika samun tafka da warwara a takardun CTC na shari’ar Kano, tsohon shugaban na NRHC ya ce abin ya wuce kuskure.
Shari'ar zaben Kano ba kuskure ba ne
"Sam ba tuntuben alkalami ba ne, akwai doka a aikin shari’a da ake amfani da ita wajen kuskuren alkalami.
Ana kiran ta dokar tuntube, misali idan za a rubuta Wi-Fi sai aka rubuta Wi-Fe, za a iya gyara wannan kuskure.
Kotu za ta sanar da wadanda ake shari’a da su, sai a gyara.
Amma ba za ta yiwu ka ce a biya ni wasu kudi kuma sai ka dawo ka ce za a gyara, dayan bangaren ne zai biyya.
Ko kuwa a ruguza hukuncin karamar kotu a rubuce sai kuma daga baya a ce kuskure ne, ba zan yarda ba.
Wadannan ikirari ne, hukuncin kotu aka zartar, yadda za a warware matsalar ita ce sake duba shari’ar idan da lokaci.
Ko kuwa ayi nazarin shari’ar kafin a tafi kotun koli. Wannan ba kuskuren alkalami ba ne, abin da aka koya mani kenan.
- Chidi Odinkalu
Bulama Bukarti wanda lauya ne da yake kasar waje, ya ce tun da yake karatun ilmin shari’a bai taba cin karo da irin wannan katabora ba.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa, lauyan ya soki yadda aka yi wannan kuskure da ya ce ba zai gyaru ba duk da yarda APC ta yi nasara.
Lauya ya ce an tsige Gwamnan Kano
An ji labari cewa wani lauya mai kare hakkin jama’a ya yi bayanin abin da ya jawo sabani a takardun hukuncin zaben Gwamnan na Kano.
Abba Hikima ya ce gaskiyar magana ita ce Gwamna bai iya samun nasara a kotun daukaka kara ba duk da kuskuren da yake cikin CTC.
Asali: Legit.ng