Kano: Takardar CTC ta nuna Kotun Daukaka Kara Ta tabbatar da Nasarar Gwamna Yusuf, Femi Falana

Kano: Takardar CTC ta nuna Kotun Daukaka Kara Ta tabbatar da Nasarar Gwamna Yusuf, Femi Falana

  • Hukuncin kotun daukaka kara a shari'ar Gwamna Abba Yusuf na Kano ya haddasa cece-kuce da muhawara a tsakanin bangaren shari’a
  • Bayanan da Femi Falana ya yi a baya-bayan nan ya kalubalanci tunanin jama’a tare da yin kira da a yi nazari sosai a kan sarkakiyar da ke tattare da hukuncin kotun daukaka karar
  • Kwafin takardar CTC da Falana ya yi nuni da shi a wata hira na baya-bayan nan, ya kara dagula dambarwar shari’a a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Babban lauyan Najeriya kuma lauya mai kare hakkin dan adam, Femi Falana, ya sake tsoma baki a hukuncin kotun daukaka kara da ya kai ga tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

NNPP ta aika sako ga NJC kan hukuncin kotun daukaka kara na korar Gwamna Abba na Kano

Femi Falana ya ce takardar CTC na kotun daukaka kara ta tabbatar da Zaben Abba Yusuf na Kano
Femi Falana Ya Yi Muhimman Bayanai Kan Takardar CTC Na Zaben Kano: “An Tabbatar da Zaben Abba Yusuf” Hoto: @Kyusufabba, Femi Falana
Asali: Twitter

A wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, Falana ya yi adawa da tunanin da jama'a ke yi na cewa an tsige Gwamna Yusuf, yana mai cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da zaben Yusuf tare da amanna da duk abun da gwamnan ya nema.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Falana ya bayyana cewa bayan ya karanta kwafin takardar CTC na hukuncin, ya yi mamakin ganin cewa yawancin hukuncin da aka yanke ya soke hukuncin karamar kotun zabe sannan aka mika nasara ga Gwamna Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban lauyan ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a shirin Arise News a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba.

Falana ya ce:

''Za ku yi mamaki idan na nuna muku hukuncin. Abin da ya ba ni mamaki shi ne, yawancin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a Kano, ya tabbatar da karar da aka daukaka, inda ya soke hukuncin da karamar kotun zabe ta yanke, tare da mika nasara ga gwamnan da karamar kotun zaben ta tsige. Akwai sabani da kotun ba za ta iya ba da bayanansu ba amma akwai yiwuwar kotun koli ta yi hukunci a kansu.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Abba

“Sabanin abun da aka nunawa jama'a, yawancin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya tabbatar da cewa hukuncin da karamar kotun zabe ta yanke ba daidai ba ne, kuma ta jingine shi a rubuce, kuma ta tabbatar da karar da aka daukaka, tare da bayar da dukkanin sassaucin da Gwamna Abba ya nema. Don haka, ka tambayi kanka, me ke faruwa?''

Yan sanda sun kama masu zanga-zanga

A wani labarin, mun ji cewa yan sanda su yi nasarar cafke wasu mutane da aka samu suna zanga-zanga a kan hukuncin zaben gwamna na jihar Kano.

Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa mutane bakwai suna hannun jami’an ‘yan sanda saboda sun fita zanga-zanga a kan tituna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng