Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Zaben Gwamnan APC, Ta Bayyana Mai Nasara
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Bassey Otu a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar Kuros Riba
- Kotun har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sunday Onor saboda rashin gamsassun hujjoji
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar PDP da ke birnin Calabar da ke jihar Kuros Riba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kuros Riba - Kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar Gwamna Bassey Otu na jam'iyyar APC.
Kotun wacce ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Otu na jihar Kuros Riba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Laraba 22 ga watan Nuwamba inda ta yi watsi da korafin dan takarar PDP, Sunday Onor, cewar Daily Post.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onor ya sake rashin nasara ne bayan kotun zabe a ranar 26 ga watan Satumba a birnin Calabar ta yi watsi da shi saboda rashin gamsassun hujjoji.
Babbar kotun a yanzu ta sake tabbatar da hukuncin karamar kotun inda ta yi fatali da korafe-korafen jam'iyyar PDP, cewar The Nation.
Gwamna Otu yayin da ya ke martani kan nasarar da ya samu ya nuna jin dadinsa inda ya ce wannan nasarar mutanen jihar ce.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Emmanuel Ogbeche inda ya ce ya na fatan hakan zai kawo karshen shari'ar.
Martanin wani dan PDP kan hukuncin kotun
Wani mazaunin Calabar, Muhammad Hussaini ya ce duk da cewa shi dan PDP amma ya ji dadin martanin Gwamna Otu na neman hadin kan 'yan adawa.
Ya kirayi sauran jam'iyyu da su hada karfi da karfe don ciyar da jihar Kuros Riba gaba.
Kotun daukaka kara a rusa zaben Zamfara
A wani labarin, kotun daukaka kara ta rusa zaben gwamnan jihar Zamfara inda ya ayyana shi wanda bai kammala ba.
Kotun ta umarci sake zabe a wasu kananan hukumomi guda uku a jihar saboda tafka magudi a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Asali: Legit.ng