2023: Mataimakin Kakakin Majalisar Kaduna da Wani Mamba Sun Sauya Sheka Daga APC

2023: Mataimakin Kakakin Majalisar Kaduna da Wani Mamba Sun Sauya Sheka Daga APC

  • Manyan mambobin majalisar dokokin jihar Kaduna sun sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa LP
  • Yan majalisan sune mataimakin kakakin majalisar, Isaac Auta Zankai, da Hanarabul Suleiman Dabo
  • Jam'iyyar LP a jihar Kaduna na kyautata zaton samun dubunnan kuri'u daga kudancin jihar

Kaduna - Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Isaac Auta Zankai da wani mamba wai wakilar Zasria, Suleiman Dabo sun sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Labour Party (LP).

Mataimakin kakakin majalisar ne mai wakiltar mazabar Kauru.

Babban Sakataren kasa na jam'iyyar LP, Umar Farouk Ibrahim, ya sanar da hakan yayin rantsar da yan kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Kaduna ranar Alhamis, 12 ga Junairu.

Ibrahim ya lashi takobin cewa rabin yan majalisar dokokin jihar na tare Peter Obi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP

Kaduna assembly
2023: Mataimakin Kakakin Majalisar Kaduna da Wani Mamba Sun Sauya Sheka Daga APC
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta ruwaitoshi da cewa:

"Maganar gaskiya itace, yau na daga cikin ranaku mafi farin ciki a rayuwana. Na zagaye kamfen wa dan takarar shugaban kasanmu, Ni da Peter Obi mun samu kyakkyawan tarba."
"Gaba daya Arewa, bamu da manya da suka sauya sheka daga APC suka shigo Labour Party kamar Kaduna inda mataimakin kakakin majalisa da wani mamba na Zaria suka sauya sheka."

Sakataren jam'iyyar ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su hada karfi da karfe saboda samun nasara a zabe mai zuwa.

A taron, dan takaran gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023, Jonathan Asake, ya gabatar da jawabinsa.

Ya bayyana cewa wajibi ne al'umma su zabi Peter Obi a zabe mai zuwa a matsayin shugaban kasa.

Yace:

"Wannan kira ne ga bautar kasa saboda kowa na son Labour Party ta kwace mulki. Matasa sun shirya kwace jihar Kaduna da Najeriya saboda Najeriya ta dawo kasa mai kere-kere sabanin ciye-ciye."

Asali: Legit.ng

Online view pixel