‘Kuskuren’ Da Aka Samu a Takardun CTC Ba Ya Nufin NNPP Ta Yi Nasara a Kotu, Lauya

‘Kuskuren’ Da Aka Samu a Takardun CTC Ba Ya Nufin NNPP Ta Yi Nasara a Kotu, Lauya

  • Magoya bayan NNPP suna murnar an ba su gaskiya wajen rubuta hukuncin shari’ar Kano
  • Abba Hikima ya ce hukuncin kotun daukaka kara bai canza ba, an yi watsi da korafin NNPP
  • A cewar lauyan, a doka da aikin shari’a ba a zabar wani bangare na hukunci a karanta shi kadai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Abba Hikima ya tofa albarkacin bakinsa game da ce-ce-ku-cen da ake yi a kan hukuncin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

A rubutun da ya yi a shafinsa na Facebook, masanin shari’ar ya nuna cewa tuntuben alkalami aka samu daga kotun daukaka kara.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano da mataimakinsa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shawara ga Abba Kabir Yusuf da NNPP

Hikima wanda matashin lauya da ya shahara a Kano, ya ba mutanen Abba Kabir Yusuf shawara su daukaka kara a kotun koli.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da takardar CTC da ke tabbatar da Abba a matsayin gwamnan Kano: "Kuskure ne"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan yake cewa tuntuben alkalami aka samu daga wajen malaman shari’a, kuma dokar kasa ta yi tanadi a kan wannan matsala.

Kotu ta na da damar gyara kuskurenta, abin da jam’iyyar APC ta ce za ayi hakan a yau bayan an yi ta jiran fitowar takardun CCT.

A cewar lauyan, bai kamata magoya bayan NNPP su dauki wani sashen bayanan CTC, ayi watsi da ragowar bayanan hukunci ba.

APC v NNPP: Matsayar Abba Kabir Yusuf

"A fahimtata wannan kuskure ne kotun daukaka kara tayi. Da wuya ka dauki hukuncin kotu ka karanta baka samu kuskure ba.
Ba a zabar wani bangare na hukunci a karanta a manta da sauran.
A wannan hukuncin duka sauran bangarorin hukuncin ya nuna Abba Kabir Ysuf bai yi nasara wajen daukaka kara ba.
Saboda haka, ba za a dauki wata sadara daya a tsaya a kanta ba. Wannan abu sannane ne a doka kuma doka tayi tanaji na a abunda ake kira “Slip Rule” wanda shi ne idan an samu kuskure ko tuntuben alkalami a hukunci, to kotu na iya gyara wannan kuskuren musamman idan ma’anar hukuncin ta bayyana.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Lauyoyin NNPP Sun Daukaka Kara a Kotun Koli Kan Tsige Abba

Saboda haka, gara a bawa ainihin dalilan daukaka wannan kara muhimmanci fiye da wannan."

- Abba Hikima

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Abdullahi Dahiru ya ce:

"Kowa ya yarda dole NNPP su tashi su bada himma zuwa ‘supreme court’. Amma babban kuskure irin wannan yana dada ragewa kotuna da alkalai kima kuma yana nuna kamar ana saka su ne daga waje su yanke hukunci."

Za a iya rantsar da Nasiru Gawuna

Dazu an samu labari akwai masu tunanin takardun CCT sun ce kotun daukaka ta rushe Hukuncin kotun zabe a kan tsige Gwamnan Kano.

Idan dai lauyoyin jam’iyyar NNPP ba su daukaka kara ba, za a rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sabon gwamna a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng