Kano: Jigon NNPP Ya Tona Asirin Hanyar da APC Ke Bi Don Mayar da Jihar Karkashin Ikonta Saboda 2027
- Yayin da kotu ta sake kwace kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, jigon NNPP ya bayyana dalilin hukuncin kotun
- Alhaji Abdulrasheed Adebisi ya ce jam’iyyar APC karfi da yaji take son mayar da jihar Kano karkashin ikonta
- Adebisi ya shawarci APC da Tinubu da su bar sauya hukuncin kotuna wurin mayar da nasara tasu don gudun matsala da tashin hankali
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Jigon jam’iyyar NNPP, Alhaji Abdulrasheed Adebisi ya yi gargadi ganin yadda jam’iyyar APC ke son kwace kujerar gwamna a jihar Kano.
Adebisi ya ce jam’iyyar APC ta zaku ta kwace kujerar karfi da yaji ba tare da tunanin abin da ka iya biyo baya ba, Tribune ta tattaro.
Mene jigon NNPP ke cewa kan shari'ar Kano?
Jigon ya ce jam’iyyar da kuma Gwamnatin Tarayya na amfani da kotuna don sauya hukuncin kotun da abin da mutane su ka zaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a bayyane ya ke tsarin da kotun zabe ta bi ya sha bam-ban da wanda kotun daukaka kara ta bi wurin yanke hukunci.
Idan ba a mantaba a ranar Juma’a ce kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin karamar kotu na rusa zaben Gwamna Abba Kabir na jihar Kano.
Kotun har ila yau, ta tabbatar da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, cewar Leadership.
Wane shiri APC ke yi kan shari'ar Kano?
Ya ce:
“Ya kamata masu ruwa da tsaki su san irin matsalar da sauya shari’ar zaben Kano zai jawo.
“Ko da za a sake zabe sun sani cewa Gwamna Abba Kabir ne zai sake lashe zaben gwamnan jihar Kano.”
Adebisi ya ce APC ta matsu ta kowa ce hanya ta mayar da jihar Kano karkashin ikonta karfi da yaji saboda zaben shekarar 2027 wanda hakan abin dariya ne.
Ganduje ya fadi yadda su ka nakasa Kwankwaso, Abba Kabir
Kun ji cewa, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana hanyar da su ka bi na samun nasara a zaben gwamnan jihar Kano.
Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani bayan hukuncin kotun daukaka kara a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng