Jigon NNPP Ya Dora Alhakin Tsige Gwamna Abba Kabir Kan Kwankwaso, Ya Bayyana Dalilansa

Jigon NNPP Ya Dora Alhakin Tsige Gwamna Abba Kabir Kan Kwankwaso, Ya Bayyana Dalilansa

  • A yayin da ake cigaba da tsokaci kan tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf, jigon NNPP ya bayyana matsayarsa
  • Sakataren jam'iyyar NNPP na ƙasa, ya bayyana cewa Kwankwaso ne silar tsige gwamnan na jihar Kano
  • Olaposi Oginni ya bayyana yadda tsohon gwamnan na Kano ya riƙa fatali da tsarin doka bayan ya shigo jam'iyyar NNPP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Sakataren jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na ƙasa, Olaposi Oginni, ya ɗora laifin tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf kan Rabiu Musa Kwankwaso.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda halastaccen wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Kano.

An dora alhakin tsige Gwamna Abba kan Kwankwaso
Jigon NNPP ya ce Kwankwaso ne ya jawo aka tsige Gwamna Abba Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Sai dai, bayan nasarar gwamnan yanzu kuma ya kamo hanyar yin bankwana da kujerarsa, idan har bai yi nasara ba a kotun ƙoli biyo bayan tsige shi da kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana kan tsige Gwamna Abba, Oginni ya ce Kwankwaso ne sila da ya jawo aka tsige gwamnan, inda ya zarge shi da yin ba daidai ba da tafka maguɗin zaɓe, cewar rahoton PM News.

Oginni ya kuma ɗora laifin halin da Gwamna Abba ya tsinci kansa a ciki a kan Kwankwaso bisa ƙwadayinsa na neman mulki ta kowane hali.

Jigon na NNPP, a cikin wata sanarwa, ya cigaba da cewa rashin tsarin dimokuradiyyar cikin gida da ake zargin Kwankwaso ne ya assasa shi ne ya jawo rashin nasara a Kano.

Kwankwaso ya lalata NNPP

A cewarsa, jam’iyyar ta yi watsi da sharuɗɗan tsarin mulki tun lokacin da Kwankwaso ya zama ɗan takarar jam’iyyar.

Ya yi zargin cewa an shigar da sunayen mutanen da ba su shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ba a fotal ɗin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a matsayin ƴan takara.

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

A cewarsa Kwankwaso da kungiyarsa ta Kwankwasiyya, sun shiga jam’iyyar NNPP ne sannan suka karɓe tsarin jam’iyyar a dukkan matakai, inda ya ce Kwankwaso ya ba da umarnin a rika ɗora sunayen ƴan takara tare ko sun yi zaɓen fidda gwani ko ba su yi ba.

Ganduje Ya Bayyana Kuskuren Abba da Kwankwaso

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana hanyar da suka bi wajen nakasa Kwankwaso da Gwamna Abba a Kano.

Ganduje ya bayyana cewa Kwankwaso ya yi kuskure inda ya shigar cikin jam'iyyar NNPP lokacin da hukumar INEC ta gama karɓar sunayen ƴan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng