Nan bada dadewa ba Matwalle zai kwato kujerar Gwamnan Zamfara, Datti

Nan bada dadewa ba Matwalle zai kwato kujerar Gwamnan Zamfara, Datti

  • Mataimakin shuugaban APC ya yi ikirarin cewa nan ba da daɗewa ba Bello Matawalle zai ƙwace kujerar gwamnan Zamfara
  • Garba Muhammad Datti ya faɗi haka ne yayin martani kan hukuncin kotun ɗaukaka kara na soke nasarar Dauda Lawal
  • Ya ayyana wannan nasara da karamin ministan tsaron ya samu da babban ci gaba a ƙoƙarinsa na kwato haƙƙinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Mataimakin shugagan APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Garba Muhammad Datti, ya ce nan ba da jimawa ba zasu kwato nasarar da jam'iyyar ta samu a zaɓen jihar Zamfara.

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Nan bada dadewa ba Matwalle zai kwato kujerar Gwamnan Zamfara, Datti Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

A rahoton Daily Trust, Datti ya ce tsohon gwamnan Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, zai ƙwato kujerarsa ta gwamna nan da ba daɗewa ba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Atiku Abubakar ya maida martani mai zafi kan tsige gwamnonin arewa biyu

Mataimakin shugaban APC ya ce hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar Jumu'a, ya ƙara masu kwarin guiwa da hangen nasara kan sakamakon da zai biyo baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba a ranar Jumu'a da ta gabata Kotun ɗaukaka ƙara ta rushe nasarar Gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP a zaben da aka yi a watan Maris.

Haka nan kuma ta ayyana zaɓen gwamnan jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammalu ba kana ta umarci hukumar zaɓe (INEC) ta shirya sabon zaɓe a kananan hukumomi uku.

Zamu kwato nasararmu a Zamfara - APC

A wata sanarwa da kakakin APC na Arewa maso Yamma, Malam Musa Mailafiya Mada, ya fitar, mataimakin shugaban APC na shiyyar, Datti ya yabawa Matawalle bisa wannan nasara.

Ya kuma bayyana nasarar da Matawalle ya samu a Kotun ɗaukaka ƙara a matsayin babban ci gaba a kokarin kwato haƙƙinsa na kujerar gwamnan Zamfara.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

A cewarsa, wannan nasarar ta tabbatar da ƙorafin APC kan nasarar da jam'iyyar PDP ta samu a Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, rahoton Daily Post.

Datti ya ƙara da bayanin cewa hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara wanda ya tabbatar da kuskuren kotun zaɓe, ya ƙara nuna alamar zahiri cewa kotu ce gatan mara galihu.

Gwamna Alia ya samu nasara a Kotu

A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar jam'iyyar PDP ta ɗan takararta kan zaɓen gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia.

Yayin yanke hukunci, kwamitin kotun ya tabbatar da nasarar Gwamna Rabaran Alia na APC a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262