Da Hannun Tinubu, Dan Takarar Gwamnan Kogi Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Garzaya Kotu Neman Hakkinsa
- Dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka ya yi amai ya lashe bayan shigar da kara kotu kan zaben Kogi.
- Ajaka shi ne ya kasance na biyu a zaben bayan sanar da sakamakon zaben da INEC ta yi a jihar
- Wannan na zuwa ne bayan dan takarar jam'iyyar APC, Usman Ododo ya lashe zaben gwamna a jihar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Jami'yyar SDP ta kasa ta yi fatali da sakamakon zaben jihar Kogi inda ta garzaya kotu don neman hakkinta.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP a jihar Kogi, Murtala Ajaka a baya ya ce ba zai bata lokacinsa wurin zuwa kotu ba duk da tafka magudi da aka yi a zaben.
Na nawa Ajaka ya kasance a zaben?
Dan takarar jam'iyyar APC, Usman Ododo shi ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajaka na jam'iyyar SDP shi ya zamo na biyu yayin da Dino Melaye na jam'iyyar PDP ya biyo shi a baya a matsayin na uku.
Duk da matakin da Ajaka ya dauka, uwar jam'iyyar ta ce ba ta yadda da wannan sakamakon zaben ba kuma za ta nemo hakkinta a kotu.
Ta ce Ajaka ne ya ci wannan zabe da aka gudanar inda ta ce ya kamata hukumar zabe ta INEC ta ayyana shi a matsayin mai nasara.
Mene shugaban jam'iyyar ke cewa?
Shugaban jam'iyyar, Alhaji Shehu Gabam ya ce tuni su ka shigar da kara inda su ke tuhumar hukumar zabe wanda har yanzu ba ta yi martani ba.
Gabam wanda ya samu rakiyar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da dan takarar gwamna da kuma mataimakinsa sun nuna damuwa kan zaben.
Ya ce sun gargadi Shugaba Tinubu kan irin wannan tsari da su ke son mayar da kasar mulkin jam'iyya daya, Daily Times.
Kungiyar ta nemi a kama Melaye
A wani labarin, wata kungiya ta bukaci jami'an tsaro da su kama dan takarar jam'iyyar PDP, Dino Melaye kan zargin ta'addanci.
Kungiyar na zargin Melaye da ta da tarzoma wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a 2007.
Asali: Legit.ng