Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Jonathan Ya Faɗi Abin da Zai Yi da Gwamna Diri Ya Sha Kaye

Zaɓen Gwamnan Bayelsa: Jonathan Ya Faɗi Abin da Zai Yi da Gwamna Diri Ya Sha Kaye

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kai wa Gwamna Duoye Diri ziyarar ban girma dangane da sake zaɓensa da aka yi karo na biyu
  • Jonathan ya ce da Diri bai sake lashe zaɓensa ba, da ya mayar da mahaifiyarsa daga Otueke zuwa Abuja
  • Ya ƙara da cewa sake zaɓen Diri na nufin jihar Bayelsa za ta fi zaman lafiya saboda gwamnan yana magance matsalar rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Yenagoa, jihar Bayelsa - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana abin da zai yi wa mahaifiyarsa idan da Gwamna Duoye Diri na jam'iyyar PDP ya faɗi zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Jonathan ya ce da ya mayar da mahaifiyarsa daga Otueke, garinsu zuwa babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Jonathan ya yi shirin mayar da mahaifiyarsa Abuja
Jonathan ya yi shirin mayar da mahaifiyarsa Abuja da Gwamna Diri ya faɗi zaɓen Bayelsa Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamna Diri a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sake zaben Diri na nufin jihar Bayelsa za ta fi zaman lafiya saboda gwamnan yana magance matsalar rashin tsaro.

Jonathan ya yaba wa Gwamna Diri

A cewar Jonathan, da an yi asarar nasarorin da aka samu wajen daƙile matsalar rashin tsaro da Diri ya faɗi zaɓen na ranar Asabar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

A kalamansa:

"Babu wani abu da zai sa jihar ta koma baya. Ya kamata mu yi tunani game da cigaban jihar tun daga batun zaman lafiya da tsaro a jihar wanda a cikin wannan shekaru uku da suka gabata, an samu cigaba sosai ta fuskar ƙungiyoyin asiri da garkuwa da mutane da dai sauransu."

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Imo: Ɗan takarar LP Achonu ya bayyana matsayarsa kan batun amincewa da shan kaye

"Ina cewa kafin zaɓen nan idan Diri ya faɗi zaɓen nan, da na mayar da mahaifiyata Abuja."

Yayin da yake ba da labarin yadda aka yi garkuwa da ɗan uwansa aka kashe shi, Jonathan ya ce:

"An yi garkuwa da ɗan uwana sau biyu a ɗaya daga cikin waɗannan lokutan, an kashe ɗaya daga cikin ƴan uwana mai suna Solo, saboda sun jefa shi cikin kogi kuma bai san yadda ake yin iyo ba."

Jonathan Ya Marawa Diri Baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana ɗan takarar da yake marawa baya a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Jonathan ya bayyana cewa yana tare da Gwamna Duoye Diri na PDP wanda yake neman yin tazarce a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng