Zaben Bayelsa: Sylva Na APC Ya Kai Ziyarar Taya Murna Ga Gwamna Diri? Gaskiya Ta Bayyana

Zaben Bayelsa: Sylva Na APC Ya Kai Ziyarar Taya Murna Ga Gwamna Diri? Gaskiya Ta Bayyana

  • Batun cewa Timipre Sylva ɗan takarar APC a zaɓen gwamnan Bayelsa ya ziyarci Gwamna Douye Diri bayan ya sha kaye a zaɓen ƙarya ne
  • Gwamna Diri, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen, an nuna shi a bidiyon yana musabaha da tsohon ministan
  • Bidiyon ya yi nuni da cewa ɗan takarar jam’iyyar APC ya kai ziyarar taya murna ga gwamnan, amma bincike ya nuna cewa an fara saka bidiyon a yanar gizo watanni shida kafin zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Yenagoa, Bayelsa -Timipre Sylva, ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan da aka kammala a jihar Bayelsa, an gan shi a faifan bidiyo yana musabaha da Gwamna Douye Diri, na jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamnan Imo: Ɗan takarar LP Achonu ya bayyana matsayarsa kan batun amincewa da shan kaye

Mutanen da suka yaɗa bidiyon a shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa ɗan takarar na jam’iyyar APC yana taya murna ne ga gwamnan wanda ya doke shi a zaɓen ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Sylva bai ziyarci Gwamna Diri ba
Timipre Sylva bai ziyarci Gwamna Diri ba bayan shan kashi a zaben gwamnan Bayelsa Hoto: Timipre Sylva, Duoye Diri
Asali: Twitter

Diri ya doke Sylva a zaɓen gwamnan Bayelsa

Ku tuna cewa Sylva, wanda ya samu ƙuri’u 110,108 a zaɓen, ya sha kaye a hannun Gwamna Diri, wanda aka sake zaɓensa da ƙuri’u 175,196.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi ta tsokaci a kan bidiyon a shafukan sada zumunta musamman a Twitter.

Wani mai amfani da shafin Twitter ya rubuta a jikin bidiyon cewa:

"Cif Timipre Sylva, ɗan takarar APC, ya kai ziyarar taya murna ga Gwamna Douye Diri na PDP. Don Allah kada ku mutu a yaƙin su. Ka yi tunanin wadanda suka rasa rayukansu a banza. Gaskiya abun baƙin ciki ne."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan kujerar sakatarenta na kasa

Tushen bidiyon inda Sylva ya ziyarci Diri

Bayan gudanar da cikakken binciken hoton baya akan bidiyon taya murnar da ake magana a kai, ya bayyana cewa wani shafi na TikTok mai amfani da sunan GbaramatuVoiceTV ya fara sanya shi.

Shafin na GbaramatuVoiceTV ya wallafa bidiyon ne a watan Mayun 2023, watanni shida kafin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

A cewar GbaramatuVoiceTV, "Mai girma Timipre Sylva ya halarci jana'izar mahaifin mai girma Douye Diri a Sampou."

Hakan ya nuna cewa faifan bidiyon tsohon ne kuma bai da alaƙa da batun zaɓen.

Dalilan Rashin Nasarar Sylva

A wani labarin kuma, mun tattaro muku dalilan da suka taka rawar gani wajen rashin nasarar Timipre Sylva a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

Daga cikin dalilan da suka jawo rashin nasara ga ɗan takarar na APC dai har da ɗauko tsohon tsageran Neja Delta a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel