Martanin Yan Najeriya Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Matsayin Gwamnan Kano

Martanin Yan Najeriya Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Matsayin Gwamnan Kano

  • Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun zabe da ta tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan jihar Kano
  • Kwamitin kotun ya kuma tabbatar Nasir Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris
  • Yan Najeriya sun yi martani kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga kujerarsa, a ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Kwamitin kotun ya tabbatar da hukuncin da kotun zaben gwamnan jihar ya yanke a ranar 20 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

Kotun daukaka kara ta tsige Abba Kabir Yusuf daga kujerara gwamnan Kano
Martanin Yan Najeriya Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Matsayin Gwamnan Kano Hotoo: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Jim kadan bayan yanke hukuncin, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya garzaya shafinsa a dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) don yin bushara da zuwan Nasir Gawuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gawuna wanda ya kasance dan takarar APC a zaben na ranar 18 ga watan Maris shine wanda kotun ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe.

Bashir ya rubuta a shafinsa:

"GAWUNA YA ISO.
"Kotun daukaka kara ta yanke hukuncinta a yau, tana mai yin fatali da shari'ar Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da tabbatar da hukuncin kotun zabe cewa Dr. Nasir Gawuna ne zababben gwamnan jihar Kano. Alhamdulillah!

Abun da yan Najeriya ke fadi kan hukuncin kotu da ya tsige Abba gida-gida

Yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi domin tofa albarkacin bakunansu a kan wannan hukunci na kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Wane hali ake ciki a birnin bayan kwace kujerar Abba Kabir da kotun daukaka kara ta yi?

@Moh_Serlis ya yi martani:

"Insha Allah Ranar Lahira sai Anyi maka Hukunci dai dai da wanda kotun zabe da kotun daukaka kara sukayi wa Abba."

@AdermuAM ya ce:

"Duk mai goyon bayan zalunci Allah ka tsine mashi alfarmar wannan rana ta Juma.a ."

@garbadaru ya yi martani:

"Ku da kanku kunsan ABBA NE YACI ZAPEN KANO. KUMA DUK SAI ALLAH YA STAYAR DAKU KUNYI BaYANI. Da duk wanda ya goyi bayan rashin gaskiya da wanda yayi murn da."

@Tasallalanee ya ce:

"Allaahu Akbarr: Muna addu'ar Allaah Ta'Alah yay riko da hannayenmu In-Shaa-Allaah ABBA KABIR YUSUF Kaine da Farin cikin domin zalinci baya dorewa kuma duk wanda ya san meye YANCI baya mamakin ganin irin wannan hukuncin, domin kowa yasan daidai..."

@Danlamiktn ya ce:

"Bai kamata idan anyi sharri ku rika fadin alhamdulillah ba."

@Elyakub02 ya yi martani:

"Kuji tsoro Allah."

@azeezsport36:

"Da azzalumae d masu goyon bayan zalunci allah k hanasu rahamar ka ta dunia data lahira."

Kara karanta wannan

Hukuncin Kano da Zamfara: APC ta yi martani yayin da kotun daukaka kara ta tsige Abba Gida Gida

@Ibrahimfatahy:

"Ya Allah darajar sayadina rasulullahi duk Wanda yake da hannu wajen cutar da mutanen Kano ko ai murana da wannan hukuncin alhalin Yana da yakinin cewa Abba ka."

Legit Hausa ta zanta da wasu mazauna jihar Kano don jin yadda suka karbi wannan hukunci na kotu da ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Muhammad Suwidi ya ce:

“Abu idan aka ce kotu babu abun da mutum ya iya, amma magana ta gaskiya Abba ne zabinmu mu Kanawa kuma kowa ya san shine ya ci zabe. Idan an yi mana fin karfi ai ba a isa ayi wa Allah ba.”

Zainab Ummi kuwa cewa ta yi:

“Sai dai muce Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, amma har ga Allah ban ji dadin wannan hukunci ba. Kawai dai an tauye mana hakki ta hanyar canja mana wanda muka zaba.”

Abba ya yi kira gabannin hukuncin kotu

A baya mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ba mutane shawara su kwantar da hankalinsu kuma su guji yin duk abin da zai iya zama sabawa doka.

A yammacin ranar Alhamis, Punch ta ce Kwamishinan yada labarai na Kano, Alhaji Baba Dantiye ya yi wannan kira a wani jawabi da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel