Shari’ar Zabe: Jam’iyyar APC Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotun da Ta Rusa Zaben Gwamnan Arewa

Shari’ar Zabe: Jam’iyyar APC Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotun da Ta Rusa Zaben Gwamnan Arewa

  • A karshe, jam'iyyar APC ta yi martani kan hukuncin kotun shari'ar zaben jihar Zamfara da aka yanke a jiya
  • Sakataren jam'iyyar, Yusuf Idris ya yabawa bangaren shari'ar kasar inda ya ce sun ji dadin wannan hukuncin adalci
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun ta rusa zaben wasu kananan hukumomi uku inda ta ce za a sake zabe

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi martani kan hukuncin kotun shari'ar zaben gwamnan jihar Zamfara.

Jam'iyyar ta ce wannan hukunci ya yi daidai inda ta ce ta yi wa Allah godiya kan wannan hukunci na adalci, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Malami ya yi hasashen abin da zai faru bayan kotu ta sauke gwamnan Kano

Jam'iyyar APC ta yi martani kan hukuncin kotun zaben jihar Zamfara
Jam’iyyar APC Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Zaben Zmafara. Hoto: Abdullahi Ganduje.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Idan ba a mantaba a jiya Alhamis kotun daukaka kara ta yi hukunci inda ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta rusa zaben kananan hukumomi uku inda ta ba da umarnin sake zabe a wadannan wurare da abin ya shafa.

Martanin APC na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam'yyar, Yusuf Idris ya fitar, Peoples Gazette ta tattaro.

Ya ce wannan hukunci na kotu ya yi musu dadi kuma su na godiya ga ubangiji kan wannan nasara, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar za ta samu nasara a zabukan da za a sake.

Wane martani APC ta yi kan zaben?

Sanarwar ta ce:

"Ganin yadda hukuncin kotu ya kasance a yau, muna da tabbacin gwamnan talakawa Bello Matawalle zai dawo kan kujerarshi ta gwamna.

Kara karanta wannan

'Inconclusive': Kotu ta ayyana zaben gwamnan Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba, za a sake zabe

"Wannan hukunci ya tabbatar mana da imanin cewa ubangiji ya na bai wa mulki ne ga wanda ya so."

Idris ya roki jama'ar jihar da kuma magoya bayansu da sauran mutanen kasar da su yi wa jam'iyyar addu'ar samun nasara.

Kotu ta rusa zaben Dauda Lawal

Kun ji cewa, kotun daukaka kara ta rusa zaben Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara a jiya Alhamis.

Kotun ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba inda ta umarci sake zaben a kananan hukumomi uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.