Kwankwaso Ya Dura Najeriya Saura Awanni 20 Ayi Hukuncin Shari’ar Zaben Kano

Kwankwaso Ya Dura Najeriya Saura Awanni 20 Ayi Hukuncin Shari’ar Zaben Kano

  • Jirgin Rabiu Musa Kwankwaso ya iso Najeriya a yammacin Alhamis wanda shi ne jaji-birin ranar hukuncin zaben Gwamnan Kano
  • Jagoran jam’iyyar NNPP ya je kasar Masar domin nemawa mahaddatan Kano hanyar da za su karo ilmi a jami’o’in kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT. Abuja - A ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo Najeriya daga kasar waje.

Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar a zaben 2023, Saifullahi Hassan ya tabbatar da haka a shafuka na sada zumunta.

Shari'ar Kano
Rabiu Kwankwaso ya dawo kafin shari'ar Kano Hoto: Hon Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Daga ina Kwankwaso ya dawo?

Kafin nan, Legit ta fahimci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shafe kwanaki bai kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Gida-Gida ta yi muhimmin kira kafin a shiga Kotu

A gajeren jawabin da ya fitar, Malam Saifullahi Hassan ya ce Rabiu Kwankwaso ya tafi kasar Masar ne domin wani aiki.

Abin da ya fitar da ‘dan siyasar shi ne zuwa jami’ar Al-Azhar da ke birnin Cairo domin a nemawa matasa gurbin karatu.

Tsohon Gwamnan na Kano zai dauki nauyin karatun wadanda aka yaye daga cibiyar musulunci ta Alhaji Musa Saleh.

Sanarwar ta ce baya ga haka, ‘dan siyasar ya yi abubuwan da ba a rasa ba yayin da ya shafe kwanaki a kasar Larabawan.

Sanata Kwankwaso ya iso babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke garin Abuja ne da kimanin karfe 2:00 na rana.

Daga cikin wadanda su ka tarbo sa a tasha akwai mukarabbai da masoya irinsu Shehu M. Bello da Yahaya Kwankwaso.

Abba zai kai Kanawa 150 kasar waje

Yayin da za a yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan Kano, yau kuma za a tura wasu matasa karatu a jamo’in kasashen waje.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar Kano, Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata ya sanar da cewa dalibai 150 za su tafi yin digirgir a yau.

Kano: Saura kiris kotu tayi hukunci

Gwamnatin jihar Kano ta fitar da jawabi inda aka ji Abba Kabir Yusuf ya na so jama’a su zauna lafiya yayin da za ayi hukunci a yau.

Duk yadda zaman kotun daukaka kara ya kasance, gwamnati ta ce a guji tarzoma, kuma ana so jami’an tsaro su ribanya kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng