Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Yi Muhimmin Kira Kafin a Shiga Kotu

Shari’ar Zabe: Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Yi Muhimmin Kira Kafin a Shiga Kotu

  • Gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwa na musamman kafin kotu ta zauna domin hukuncin shari’ar zaben Gwamna na 2023
  • Abba Kabir Yusuf ya roki jama’a su guji duk abin da zai jawo rikici a Kano, ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan yada labarai
  • Wata kungiya ta WAI ta yi makamancin wannan kira a makon nan, an kuma bukaci jami’an tsaro su tabbatar da tsaro a jihar Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ba mutane shawara su kwantar da hankalinsu kuma su guji yin duk abin da zai iya zama sabawa doka.

A yammacin ranar Alhamis, Punch ta ce Kwamishinan yada labarai na Kano, Alhaji Baba Dantiye ya yi wannan kira a wani jawabi da ya fitar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya dura Najeriya saura awanni 20 ayi hukuncin shari’ar zaben Kano

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto:Na Ƴar Talla (Na Ƴar Talla
Asali: Facebook

Baba Dantiye ya ce shawarar ta zama dole ne ganin cewa wasu bata-gari za su iya amfani da damar shari’ar zabe, su kawo rikici a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kabir Yusuf v Nasiru Gawuna a kotu

Ganin a yau ne kotun daukaka kara za ta raba gardama tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinan ya yi magana.

Kamar yadda Solacebase ta fitar da rahoto, A cewar Dantiye, akwai bukatar a zauna lafiya domin cigaban jihar Kano da kuma daukacin kasa.

Har ila yau, jawabin kwamishinan ya kunshi kira ga jami’an tsaro su kara kokari wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya da aminci.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuma bukaci a kare lafiya da dukiyoyin al’ummar Kano.

Jawabin ya fito ne ta bakin Mai taimakawa Kwamishinan wajen harkoki na musamman, Sani Abba Yola, Vanguard ta fitar da rahoton.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun haramta murna ana shirin yanke hukunci a shari’ar zaben gwamna

Shari'ar zabe: Kiran WAI ga mutanen Kano

Ana haka sai aka ji wata kungiya mai yaki da rashin adalci a Kano mai suna WAI, ta yi kira ga mazauna su rungumi hukuncin da za a zartar.

A wani jawabi da ya fito ta ofishin shugaban WAI, Umar Ibrahim Umar, an nemi mutane su guji tada tarzoma ko duk wani nau’i na hayaniya.

Duk yadda hukuncin ya kasance, Umar Ibrahim Umar ya roki jama’a su zauna lafiya.

Jami'an tsaro a Bauchi da Kao

Kafin a yanke hukunci a kotu, rahotanni sun zo cewa 'yan sanda sun dauki matakai a Bauchi kamar yadda aka yi a Jihar Kano tun kafin yanzu.

'Yan sanda sun ja kunnen ‘yan siyasa musamman magoya bayan APC, PDP daNNPP ganin za ayi hukunci kan zaben Gwamnonin Kano da Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng