Zamfara: Shin Gwamna Dauda Ne Ya Dauki Nauyin Lauyoyin Atiku kan Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Zamfara: Shin Gwamna Dauda Ne Ya Dauki Nauyin Lauyoyin Atiku kan Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi watsi da rade-radin da ke zargin cewa Gwamna Lawal Dauda ne ya dauki nauyin lauyoyin Atiku Abubakar a shari'arsa da Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Kungiyar jam'iyyar APC mai mulki karkashin inuwar ARHIN ce ta yi watsi da wannan zargin
  • Kungiyar masu rajin kare dimokradiyya ta bayyana zargin a matsayin wani yunkuri na lalata alakar da ke tsakanin Shugaban kasa da Gwamnan Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Kungiyar jam'iyyar APC karkashin inuwar ARHIN ta yi gargadi kan boyayyen shirin da wasu magauta ke yi domin haddasa gaba tsakanin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Karkashin jagorancin Mal. Danjuma Umar, kungiyar ta tabbatar da cewa wadanda ke kulla-kullan suna neman jan hankali ne kuma suna da nasaba da yan siyasar da ake bincike kansu yanzu haka saboda ayyukan damfara.

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

An gano ba Lawal bane ya dauki nauyin lauyoyin Atiku ba
Zamfara: Shin Gwamna Dauda Ne Ya Dauki Nauyin Lauyoyin Atiku Kan Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Atiku Abubakar/Dauda Lawal/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da aka aikewa jaridar Legit a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, kungiyar ta jaddada cewa Gwamna Lawal bai da hannu a yunkurin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP na son tabbatar da sahihancin takardar Shugaba Tinubu na jami'ar jihar Chicago.

Sanarwar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wanene ya dauki nauyin shari'o'in Atiku kafin zuwa Dauda Lawal harkar siyasa? Shin Dauda ne kadai gwamnan PDP a Najeriya? Wadannan sune tambayoyi ga wadanda ke ganin cewa ta hanyar bata sunan Dauda da alakar shugaban kasar ne, za su iya cin bulus a damfararsu."

Badakalar CSU: Kungiyar APC ta goyi bayan Gwamna Dauda, ta yi watsi da zargin daukar nauyin shari'ar Atiku

Bugu da kari, kungiyar ta yi watsi da ikirarin cewa Gwamna Lawal ne ya dauki nauyin tawagar lauyoyi Atiku Abubakar ta bangaren kudi, inda ta bayyana lamarin a matsayin kanzon kurege.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

Kungiyar ta ce:

"Kundin tsarin mulkin Najeriya na fushi da zamba, kuma wadanda aka samu da hannu a ciki ba mutane ne da za a damkawa ragamar shugabanci ba.
"Ba laifi bane don Atiku Abubakar ya nemi doka ta tabbatar da gaskiya, kuma kada a kullaci wadanda suka goya masa baya a matsayin wadanda za a yi wa bita da kulli.

ARHIN ta kuma bayyana makircin tsohon Gwamna Matawalle da hadimansa na son ware jihar Zamfara daga tsakiyar gwamnati ta hanyar hana mai girma gwamna ganawa da Shugaban kasar.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da wannan matakin da cewa ba wai rashin tausayi bane kawai, har ma da cutar da ci gaban al’ummar jihar Zamfara da ke ci gaba da farfadowa daga kalubalen rashin tsaro da talauci.

ta yi kira ga shugaba Tinubu da ’yan Najeriya da su yi watsi da irin wadannan jita-jita marasa tushe, sannan su maida hankali wajen gina Najeriya mai karfin tattalin arziki da wadata.

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Gagdi ya karyata neman a binciki Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kwamitin sojojin ruwa a majalisar taraya, Yusuf Adamu Gagdi ya musanya batun bincike a kan Bola Ahmed Tinubu.

The Guardian ta rahoto Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya na cewa babu inda ya fito ya ce za a binciki shugaban kasa game da kudin tallafin fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng