Majalisa Ta Rantsar da Sabon Sanatan PDP da Kotun Daukaka Kara Ta Bai Wa Nasara
- Sabon sanatan PDP, Austin Akubundu ya karbi rantsuwa a yau Laraba 15 ga watan Nuwamba a Majalisar Dattawa da ke Abuja
- Akobundu ya samu nasarar zama sanata ne bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben Abia ta Tsakiya
- Har ila yau, kotun ta kwace kujerar sanata mai ci Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP kan tafka magudi a zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta rantsar da Austin Akobundu na jam'iyyar PDP da ke wakiltar Abia ta Tsakiya a Majalisar.
Legit Hausa ta ruwaito cewa kotun daukaka kara ta bai wa Akobundu nasara bayan ya kalubalanci nasarar dan jam'iyyar LP.
Wane hukunci kotun ta yanke a baya?
Kotun ta kwace kujerar dan takarar na jam'iyyar LP, Darlington Nwokocha saboda kura-kurai da aka samu a yayin gudanar da zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta rantsar da Akobundu ne a yau Laraba 15 ga watan Nuwamba a dakin Majalisar da ke birnin Tarayya Abuja, cewar Channels TV.
Sabon sanatan da aka rantsar, ya kasance tsohon Kanal din soja da ya yi ritaya wanda kuma ya rike mukamin karamin Ministan Tsaro.
Wasu mukamai Akobundu ya rike a baya?
Har ila yau, Akobundu ya taba rike mukamin sakataren tsare-tsare na jam'iyyar PDP a matakin kasa, cewar TheCable.
Bayan rantsar da Akobundu a Majalisar, jam'iyyar PDP ta na da sanata daya kenan a yankin Kudu maso Gabashin kasar.
Yayin da Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu na APC ke wakiltarsu sai kuma Abia ta Kudu wanda Enyinnaya Abaribe na jam'iyyar APGA ke wakilta.
Kotun zabe ta kwace kujerar sanatan LP
A wani labarin, kotun daukaka kara ta kwace kujerar Sanata Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP a jihar Abia.
Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan jam'iyyar PDP, Austin Akobundu a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Abia ta Tsakiya.
Wannan hukunci na kotun ya bai wa jam'iyyar PDP damar samun sanata daya tilo kenan a jihar yayin da APC da APGA ke da wakilai.
Asali: Legit.ng