Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tanadi Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC na Arewa da aka tsige
- Kotun ɗaukaka kara ta shirya, ta tanadi hukunci domin raba gardama kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Nasarawa
- A baya Kotun zaɓe ta tsige Gwamna Abdullahi Sule na APC, ta ayyana ɗan takarar PDP a matsayin zababben Gwamna
- Sai dai Gwamna Sule ya garzaya Kotun ya ɗaukaka kara kuma Alƙali ya ce za a sa ranar yanke hukunci nan gaba kaɗan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, na APC ya shigar gabanta.
Gwamnan ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ɗaukaka ƙara yana kalubalantar mafi akasarin hukuncin Kotun zabe, wadda ta tsige shi daga matsayin Gwamnan Nasarawa.
Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen Gwamnan Nasarawa ta sauke Sule kana da ayyana ɗan takarar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓe, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ɗaukaka kara zata raba gardama
Yayin zaman sauraron ƙarar da Gwamna Sule ya ɗaukaka, kwamitin alkalai uku na Kotun ɗaukaka ƙara karkashin mai shari'a Uchechukwu Onyemenam, ya ce za a sanar da ranar yanke hukunci.
Alƙalin ya shaida wa kowane ɓangare da ƙarar ta shafa cewa nan bada daɗewa ba Kotun zata faɗi ranar yanke hukunci kan sahihin wanda ya ci zaɓen Nasarawa.
Yadda zaman Kotun ya kasance
Yayin zaman sauraron ƙarar, Lauyan Gwamna Sule, Wole Olanipekun, ya roƙi Kotun ɗaukaka ƙara ta rushe hukuncin Kotun zaɓe, Channels tv ta ruwaito.
Olanipekun ya shaida wa Alƙalan cewa Kotun zaɓe ta musu rashin adalici yayin da ta ƙi karban bayanan shaidun da suka gabatar kuma ta yi watsi da alƙaluman BVAS da aka miƙa mata.
Bayan gama bayanansa, lauyan PDP da ɗan takararta Ombugadu, Kanu Agabi, ya roƙi Kotun ta kori ƙarar da aka ɗaukaka wacce ta kalubalanci hukuncin Kotun zaɓe.
Agabi, wanda ya kafa hujja da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke, ya ce a yayin da take yanke hukunci, karamar kotun ta yi cikakken bayani kan yadda ta cimma wannan matsaya.
Kotu zata yanke hukunci kan zaben Legas
A wani labarin na daban kuma Kotun daukaka kara ta fara zaman sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Lagas na 2023.
A yau laraba, 15 ga watan Nuwamba, ne kotun za ta yanke hukunci a kan shari'ar da ke neman a tsige Babajide Sanwo-Olu daga kujerar gwamnan Lagas.
Asali: Legit.ng