A Karshe PDP Ta Maye Dan Takarar Gwamna Na Imo Amma Da Sharadi Guda 1

A Karshe PDP Ta Maye Dan Takarar Gwamna Na Imo Amma Da Sharadi Guda 1

  • Jam’iyyar PDP ta sanar da Setonji Koshoedo a matsayin sabon mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, inda ya maye gurbin Samuel Anyanwu
  • Umar Damagum, wanda ya bayyana hakan, ya ce nadin da aka yi wa Koshoedo zai dakata har sai an ji sakamakon babbar kotun jihar Enugu
  • Amma Anyanwu, wanda aka hana shi bayyana kansa a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa, ya koma aikinsa a sakatariyar jam’iyyar a ranar Talata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP na kasa, ya nada Setonji Koshoedo a matsayin sakataren riko na jam'iyyar a matakin kasa.

Har zuwa nadin nasa, Koshoedo ya kasance mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan APC a jihar Arewa

Shugaban riko na jam’iyyar PDP na kasa Umar Damagum ne ya sanar da nadin bayan kammala taron NWC a ranar Talata.

Setonji Koshoedo
PDP ta nada Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa Hoto: Setonji Koshoedo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damagum ya bayyana cewa nadin Koshoedo na zai kasance har zuwa lokacin da za kammala shari'ar da ke gaban babbar kotun Enugu.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, tun da farko, babbar kotun jihar Enugu ta umarci Ayanwu, dan takarar PDP a zaben gwamna da aka kammala a jihar Imo da ya daina bayyana kansa a matsayin sakataren jam'iyyar.

PDP ta nada sabon sakataren kasa

Kotun ta kuma umarci Umar Damagum, mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP da ya amince da Sunday Udeh-Okoye a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa.

Amma Damagum, a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, ya sanar da nadin Koshoedo a matsayin sabon sakataren riko na jam’iyyar PDP na kasa bayan taron kwamitin NWC na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Zabe ya kammala a Kogi, INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe, ya fi kowa adadin kuri'u

Samuel Anyanwu ya koma aiki matsayin sakataren jam'iyyar PDP na kasa

Shugaban riko na PDP yace:

"Mun yanke shawarar cewa mataimakin sakatare na kasa ya karbi ragamar mulki har zuwa lokacin da za'a yanke hukunci a shari'ar kotun.

A ranar Talata ne dai rahotanni suka ce Anyanwu ya koma aiki matsayin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, kwanaki uku da kayar da shi a zaben gwamna da aka kammala a Imo.

A baya dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana Anyanwu bayyana kansa a matsayin sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

Dalilin da ya sanya PDP ta sha kaye a zaben gwamnan Imo

Gwamnatin jihar Imo ta ɗora alhakin rashin nasarar da jam'iyyun Labour Party da PDP suka yi a zaben gwamna da aka kammala a kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.