Zaben Kogi: INEC Ta Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Sake Zabe a Jihar Kogi, Ta Fadi Ranar da Za a Yi

Zaben Kogi: INEC Ta Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Sake Zabe a Jihar Kogi, Ta Fadi Ranar da Za a Yi

  • Yayin da ake ci gaba da zaben gwamna a jihar Kogi, hukumar zabe ta INEC ta umarci sake zabe a wasu mazabu a jihar
  • Hukumar ta INEC ta sanar da sake zaben a Unguwanni tara da ke karamar hukumar Ogori Magongo a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamako a jihar bayan kada kuri'u a jiya Asabar 11 ga watan Nuwamba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Hukumar zabe ta INEC ta umarci sake zabe a wasu Unguwanni tara a jihar Kogi.

Unguwanni taran da za a sake zaben dukkansu na karamar hukumar Ogori Magongo da ke jihar Kogi, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: a karshe, Dino Melaye ya yi martani kan dokuwa da yake a zabe, ya fadi abin da INEC za ta yi

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Lahadi 12 ga watan Nuwamba ta ba da umarnin saboda wasu kura-kurai da aka samu.

Kwamishinan zabe na hukumar, Mohammed Haruna ya ce zaben za a gudanar da zaben ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, cewar TheCable.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin fitar wasu sakamakon zabe tun kafin fara kada kuri'u a wuraren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Dadi da kari kan sanarwar da muka yi a jiya, mun samu karin bayani daga ofishinmu a jihar Kogi kan fitar sakamako kafin fara zabe.
"Wuraren da abin yafi faruwa su ne Unguwanni 10 daga cikin tara a karamar hukumar Ogori/Magongo a jihar Kogi."

Hukumar ta ce Unguwannin sun hada da Eni da Okibo da Ileteju da Aiyeromi da Ugugu da Obinoyin da Obatgben da kuma Oturu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.