Zaben Kogi: Hadimin Atiku Ya Caccaki INEC, Ya Bayyana Dalilansa

Zaben Kogi: Hadimin Atiku Ya Caccaki INEC, Ya Bayyana Dalilansa

  • Dele Momodu ya caccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan dakatar da zaɓen gwamnan Kogi a wasu gundumomi tara na jihar
  • Hadimin na Atiku Abubakar ya yi nuni da cewa abun kunya ne yadda har yanzu hukumar ba ta iya shirya zaɓe cikin lumana
  • INEC dai ta dakatar da zaɓen ne a wasu gundumomi tara na ƙaramar hukumar Ogori/Magongo kan wasu zarge-zarge

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Dele Momodu, ya mayar da martani game da dakatar da zaɓen gwamna da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi a wasu gundumomi tara na jihar Kogi.

A baya dai hukumar ta sanar da dakatar da gudanar da zabe a gundumomi tara na Ogori/Magongo, ƙaramar hukumar da a baya aka nuna damuwar cewa jami’an zaɓe sun zo da sakamakon zaɓensu.

Kara karanta wannan

Bayelsa: "Dole a dakatar da zaɓukan da ake yi bayan babban zabe" Tsohon shugaban ƙasa ya faɗi dalili

Dele Momodu ya caccaki INEC kan zaɓen Kogi
Dele Momodu ya caccaki dakatar da zaɓen da INEC ta yi a jihar Kogi Hoto: Dele Momodu Ovation, INEC Nigeria
Asali: Twitter

Dino Melaye, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen, ya yi kira ga magoya bayansa da wakilan jam’iyyarsa da su yi zanga-zanga tare da tabbatar da cewa sun ga babu komai a takardun rubuta sakamakon zaɓe kafin su fara kaɗa ƙuri’a a rumfunansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take sanar da dakatar da zaɓe a mazaɓun, INEC ta ce:

"Duk wani sakamakon zaɓe wanda ba ta hanyar zaɓe aka same shi a rumfunan zaɓe ba, ba za a amince da shi ba."

Amma da yake mayar da martani kan dakatarwar da aka yi a gundumomin da lamarin ya shafa, Momodu, jigo a jam’iyyar PDP, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, ya caccaki hukumar zabe da kasa kammala zaben a jihohi uku kacal, inda ya kara da cewa Allah ne kadai zai iya ceto ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke wajen zaɓe a Bayelsa yayin da jami'an INEC suka nemi tsira da ransu, bidiyo ya fito

A kalamansa:

"Abun kunya ne cewa har yanzu INEC ta na fuskantar irin wannan ƙalubalen zaɓen da rikici a jihohi uku kacal, wannan abun takaici ne, abun damuwa ne kuma abun kunya ne. Da alama Allah ne kawai zai iya ceto Najeriya a wannan halin."

INEC Ta Yi Martani Kan Ɓullar Sakamako

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi martani bayan ɓullar wani sakamakon zaɓe da aka cika a wasu rumfunan zaɓe a Kogi.

Hukumar ta bayyana cewa tana sane da ɓullar sakamakon zaɓen, kuma za ta ɗauki matakin da ya dace a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng