Yadda Aka Shakawa Masu Zabe N40, 000 Domin a Saye Kuri’unsu a Zaben Gwamnoni
- Mutane sun yi kasuwa a zaben Gwamnonin da aka yi musamman a kananan hukumomin Bayelsa da Imo
- Hukumar EFCC ta kama mutane 14 da ake zargi da sayen kuri’u a rumfunan zabe, za a gurfanar da su a kotu
- Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya fitar da sanarwa cewa sun karbe N11m daga hannun jama’a
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bayelsa - Masu zabe sun shaida yadda aka rika biyansu daga N12, 000 zuwa N40, 000 saboda kurum a saye kuri’unsu a jihar Bayelsa.
Rahoto ya zo daga Daily Trust wanda ya nuna kudi ya yi tasiri a zaben jihar Bayelsa.
Mai girma Duoye Diri yana so ya rike kujerarsa a PD, shi kuma babban abokin adawarsa, Timipre Sylva ya dage sai ya koma mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan takaran LP ya ce an saye kuri'u
‘Dan takaran da ya tsayawa LP a jihar ta Bayelsa a zaben bana, Udengs Eradiri ya nuna irin yadda aka saye kuri’un jama’a ya ba shi tsoro.
Da aka yi magana da shi bayan kada kuri’arsa a garin Agudama-Ekpetiama, Eradiri ya ce an tunkare shi ya saye kuri’u, amma bai yarda ba.
‘Dan takaran yake cewa abin da ya fi ba shi takaici shi ne wata mata wanda ya nauyin karatun yaronta, ta saida kuri’arta a kan N14, 000.
EFCC ta kama masu sayen kuri'a
Mutane akalla 14 aka yi ram da su, ana tuhumarsu da laifin sayen kuri’u a zaben gwamnoni da aka gudanar a Bayelsa, Imo da kuma Kogi.
Sanarwar da hukumar EFCC ta fitar ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike, za a mika duk wadanda aka kama zuwa gaban kotu.
An samu jimillar kudi har N11,040,000; N9,310,000 a jihar Bayelsa sai N1,730,000 a Imo.
Wa zai yi nasara a zaben Bayelsa?
Shi kuwa ‘dan takaran APC da ya kada kuri’a a Dukuraku da ke Okpoama a karamar hukumar Brass, ya ce duk da haka yana hango nasara.
Duk da rikicin da ya barke a wasu wurare a sakamakon zaben, Gwamna Douye Diri ya yi ikirarin an samu cigaba sosai wajen takarar bana.
Sakamakon zaben Kogi, Imo da Bayelsa
Ana da labari cewa zaben sabon gwamnan jihar Kogi yayi zafi yayin da jam’iyyun PDP da APC su ka sha gaban juna a Jihohin Bayelsa da Imo
Ahmed Usman Ododo da Murtala Yakubu Ajaka suna samun nasara a Kogi ta tsakiya da kuma Kogi ta gabas – dama nan ne yankunan da su ka fito.
Asali: Legit.ng