Zaɓen Gwamnan Jihar Kogi: Ƴan Najeriya Sun Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara
- A ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba ne ake sa ran za a gudanar da zaɓen gwamna a Kogi, inda ƴan takara 18 za su fafata
- Wani zaɓen jin ra'ayi da Legit.ng ta yi a Twitter ya yi hasashen Dino Melaye a matsayin wanda zai iya lashe zaɓen da kaso 54.4%, sai Usman Ahmed Ododo ya samu kaso 26%
- Sai dai yana da kyau a lura cewa zaɓen hasashe ne kawai, kuma INEC za ta bayyana wanda ya yi nasara a hukumance bayan an kammala kaɗa ƙuri’a
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Lokoja, jihar Kogi - Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.
Gabanin zaɓen, ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi hasashen wanda zai yi nasara a zaɓen jin ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter.
Bayanai na INEC sun nuna cewa jam’iyyun siyasa da ƴan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaɓen Gwamnan Kogi: Su waye ne manyan ƴan takara?
Ko da yake ƴan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen, huɗu daga ciki ana ɗaukar su a matsayin waɗanda ke kan gaba saboda yanayin tarihin siyasar jihar.
Waɗannan ƴan takarar su ne:
- Usman Ahmed Ododo (APC)
- Dino Melaye (PDP)
- Muritala Yakubu Ajaka (SDP)
- Leke Abejide (ADC)
Wa zai lashe zaben gwamnan Kogi? An hasashen cewa Dino Melaye zai yi nasara
A zaɓen jin ra'ayin da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter, kaso 54.4% na waɗanda suka yi zaɓen sun ce Dino Melaye, ɗan takarar jam'iyyar PDP ne zai lashe zaɓen, yayin da kaso 26% suka zaɓi Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Haka kuma, kaso 14.9% na waɗanda suka yi zaɓen sun yi hasashen cewa ɗan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Muritala Yakubu Ajaka, zai yi nasara yayin da sauran kaso 4.7% suka zaɓi Leke Abejide na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Legit.ng ta lura cewa wannan zaɓen jin ra'ayi ne kawai domin samar da haske kan yadda za a kaɗa ƙuri'a.
INEC ce za ta gudanar da cikakken zaɓe, kuma hukumar zaben za ta bayyana wanda ya yi nasara a hukumance.
An Yi Hasashen Nasara Ga Ododo
A wani labarin kuma, babban malamin addini, fasto Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen ɗan takarar da zai samu nasara a zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Faston ya yi hasashen cewa ɗan takarar jam'iyyar APC, Ahmed Usman Ododo, shi ne wanda zai samu nasara a zaɓen.
Asali: Legit.ng