"Na San Wanda Za Su Zaɓa": Jigon APC Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaɓen Gwamnan Jihar Imo

"Na San Wanda Za Su Zaɓa": Jigon APC Ya Yi Hasashen Wanda Zai Lashe Zaɓen Gwamnan Jihar Imo

  • Wani jigon jam'iyyar APC mai mulki, Francis Okoye, ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan Imo a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba
  • Okoye ya ce Gwamna Hope Uzodinma na jam’iyyar APC ne zai yi nasara kuma a sake zaɓen shi a karo na biyu
  • A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Legit.ng, ya ce mutane sun san abin da suke so kuma za su zaɓi Uzodinma saboda bajintar da ya yi a cikin shekaru 4 da suka gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Owerri, jihar Imo - Shugaban gamayyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shiyyar Kudu maso Gabas, Francis Okoye, ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa na cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya riƙe albashin ma'aikata a jihar.

Kara karanta wannan

Imo: Ɗan takarar Gwamnan PDP ya janye saura awanni a fara zaɓe? Gaskiya ta bayyana

Okoye ya ce wannan jita-jita wani yunƙuri ne da ƴan adawa suka shirya domin yi wa gwamnan baƙin fenti gabanin zaɓen ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

An hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan Imo
Jigon APC ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan Imo Hoto: Hope Uzodimma/Senator Samuel Nnaemeka Anyanwu/Senator Athan Nneji Achonu
Asali: Facebook

Sai dai ya ce hakan ba zai yi tasiri ba, domin al’ummar jihar Imo sun tabbatar da cewa gwamnan ya yi gwaninta kuma za su sake zaɓen shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Uzodinma zai yi nasara?

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman ta wayar tarho da Legit.ng.

"Na yi wannan hirar ne daga jihar Imo, na yi mu’amala da jama’ar jihar Imo kuma na tattauna da wasu ma'aikatan gwamnati kuma dukkansu sun tabbatar da cewa gwamnan ya yi abin a zo a gani kuma za su sake zaɓen shi." A cewarsa.

Mamban a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC ya ce Gwamna Uzodimma ya cika alƙawarin da ya ɗauka ta fuskar samar da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun bankaɗo wani makirci da aka ƙulla, sun yi kakkausan gargaɗi kan zaben Gwamna a jihohi 3

Jigon na APC ya ce jama’a za su saka masa da ƙuri'unsu a ranar Asabar domin sake koma wa mulkin jihar a wa'adi na biyu.

A kalamansa:

"Gwamna Hope Uzodimma ya nuna jagoranci, ya tabbatar da ƙwarewarsa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa kusan shekaru huɗu da suka wuce. Ina da tabbacin cewa al'ummar jihar Imo za su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu a ranar 11, ga watan Nuwamba, su sake zaɓensa a karo na biyu."
"Wannan shi ne mutumin da kafin ya shiga ofis a matsayin gwamna, ya samu jihar cikin wani mawuyacin hali, musamman a ɓangaren ababen more rayuwa, misali ɗauki matsalar hanyoyi, babu hanyar da za a iya bi a jihar Imo, musamman na zuwa birnin Owerri kafin zuwan Gwamna Hope Uzodinma kan mulki, amma yau za ka iya amfani da hanyoyi da dama a jihar Imo a cikin babban birnin jihar da sauran ƙauyaku."

Kara karanta wannan

"Ina kwance a asibiti na kusa mutuwa": Jigon APC mara lafiya ya koka

Okoye ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a sake zaɓen Uzodimma kan karagar mulki a karo na biyu saboda ayyukansa da jama’a ba za su iya musantawa ba.

Uzodinma da Achonu Ba Su Sa Hannu Kan Zaman Lafiya Ba

A wani labarin kuma, gwamnann jihar Imo, Hope Uzodinma da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar Labour Party, Athan Achonu, ba su sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Ƴan takarar biyu sun ƙi halartar taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyan, duk kuwa da muhimmancin da hakan yake da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng