Zaben Gwamnan Kogi: Muhimman Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar SDP, Murtala Ajaka

Zaben Gwamnan Kogi: Muhimman Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar SDP, Murtala Ajaka

Lokoja, jihar Kogi - Dan takarar gwamnan jam'iyyar SDP, Hon. Murtala Yakubu Ajaka, ya kasance fitacce a siyasar jihar Kogi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Dan siyasar mai shekaru 45 ya rike mukaman siyasa daban-daban a baya kuma ya nuna kwarewarsa wajen shugabanci ba wai a siyasa kawai ba harma a bangaren kasuwanci.

Dan takarar gwamnan Kogi a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka
Zaben Gwamnan Kogi: Muhimman Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani Game da Dan Takarar SDP, Murtala Ajaka Hoto: Murtala Yakubu Ajaka
Asali: Facebook

Yayin da mutane da mazauna jihar Kogi za su jefa kuri'u a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba don zabar sabon gwamna, akwai wasu abubuwa masu ban sha'awa game da Ajaka, daya daga cikin manyan yan takara a zaben.

Ranar haihuwa

An haifi Hon. Murtala Yakubu Ajaka a ranar 13 ga watan Fabrairun 1978, a karamar hukumar Igalamela/Odolu na jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Fatima Taiye Suleiman: Muhimman abubuwa 5 kan yar takarar gwamna mace tilo a zaben gwamnan Kogi

Karatu

Ajaka ya fara karatunsa a makarantar firamare na Roman Catholic Mission (RCM), Ajaka amma ya mallaki kwalin kammala firamare a Federal Polytechnic Staff School, Idah.

Ya yi karatunsa na sakandare a Barewa College, Zaria, a jihar Kaduna.

Dan takarar na SDP ya garzaya zuwa jami'ar Abuja, a inda ya mallaki kwalin digiri.

Harkar siyasa

Ya shiga harkar siyasa bayan ya kammala jami'a kuma mukami na farko da ya fara rikewa a siyasa shine lokacin da aka zabe shi a matsayin mataimakin sakataren jina na rusasshiyar jam'iyyar AC, reshen birnin tarayya.

Daga baya aka nada shi wakilin AC a majalisar wakilai a watan Disamba 2006.

Ya kara karfi ne a siyasa yayin da jam'iyyun ACN, ANPP da CPC suka yi maja suka zama APC a 2013 inda aka nada shi jagoran daya daga cikin kwamitocin jam'iyyar.

Babban dan kasuwa

Ba wai a iya siyasa kawai ya tsaya ba harma da bangaren kasuwanci. Ajaka ya kasance kwararren dan kasuwa wanda ke sha'awar harkar mai da iskar gas, wuta da makamashi, da bayar da shawarwari.

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

A yanzu haka shine shugaban kamfanonin Yakubens Nigeria Ltd, da MMB Petroleum and Chemical Company Ltd.

Ajaka bai janye daga tseren gwamnan Kogi ba

A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar SDP ta karyata rahotannin da ke cewa dan takararta a zaben gwamnan jihar Kogi, Murtala Ajaka ya janye daga tseren.

A cewar jam'iyyar, Ajaka ne zabin al'umma kuma ba zai janyewa kowa ba a matakin da aka kai yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng